ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kallo Ya Koma Kano: Gwamna Abba Na Shirin Rattaba Hannu Kan Sabuwar Dokar Masarautar Kano

by Abubakar Sulaiman
2 years ago
Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf, na shirin rattaba hannu kan dokar majalisar masarautu da aka yi wa kwaskwarima yayin da majalisar dokokin Jihar Kano ke ci gaba da zama a yau domin kammala dokar.

Tun a jiya ne dai jami’an tsaro suka warwatsu a duk muhimman wurare na zauren majalisar lokacin da ƙudirin dokar da ke da nufin soke kafa masarautu biyar ya tsallake karatu na farko.

  • Sanata Barau Jibrin Ya Ƙaddamar Da Motocin Zirga-Zirga A Kano
  • Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yi Wa Dokar Da Ta Tsige Sarki Sanusi II Kwaskwarima

Shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne, ya fara miƙa buƙatar yi wa dokar masarautun Kano (gyara mai lamba 2) ta 2024, manyan sauyin da ake niyyar yi zai jirkita tsarin masarautun da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a shekarar 2019.

ADVERTISEMENT

Tsohuwar dokar ta 2019 wacce ta samar da sabbin masarautun Bichi da Rano da Gaya da Ƙaraye tare da (birnin) Kano, an yi gyare-gyare da dama a cikinta, inda aka yi  kwaskwarima a baya-bayan nan a shekarar 2020 da kuma 2023.

Sashe na 3(1) na dokar ya zayyana ikon waɗannan masarautun, inda kowannensu ke da ƙananan hukumomi da dama a ƙarƙashinsu.

LABARAI MASU NASABA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Garan da aka yi a shekarar 2020 biyo bayan sauke Sarki Muhammadu Sanusi II, inda aka sake fasalin majalisar ta zama Sarkin Kano a matsayin mai jan ragamar na dindindin ga ragowar masarautun.

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Har ila yau, dokar ta bai wa gwamna, idan har majalisar Sarakunan ta amince, ya iya tsigewa ko naɗa sabon Sarkin a duk masarautun.

Yanzu haka dai garin Kano yayi jim a daidai lokacin da majalisar ke shirin yin zama na musamman domin amincewa da gyaran.

Daily Trust ta rawaito cewa; wani babban jami’i a majalisar dokokin ya jaddada cewa babu wani da zai iya dakatar da yin gyaran domin sun ƙuduri niyyar yin shi tuntuni, wanda hakan ke nuni da cewa an daɗe ana shirin yin garambawul ga tsarin masarautun.

Sai dai shugaban marasa rinjaye Abdul Labaran Madari, ya tabbatar da cewa duk da cewa ƴaƴan jam’iyyar APC ba sa adawa da gyaran da aka yi niyyar aiwatarwa, amma sun dage cewa ba za a rusa ko ɗaya daga cikin masarautu biyar ɗin ba, kuma Sarkin (birnin) Kano na yanzu, Aminu Ado Bayero shi zai ci gaba da zama a kan kujerarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin Kano da Sarkin Bichi duk ba sa gari, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan illar rashin nasu.

Majiyoyi na nuni da cewa da zarar majalisar ta zartar da ƙudirin, nan take Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanya mata hannu, wanda hakan wataƙila zai iya maido da Sarki Sanusi II.

Sarki Muhammadu Sunusi II
Sarki Muhammadu Sunusi II
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi
Hotuna

HOTUNA: Yadda Tinubu Ya Kai Ziyara Don Ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi

December 20, 2025
Next Post
Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.