Daga Abubakar Abdullahi, Lafia
An kalubalanci manoman Jihar Nasarawa da su rungumi ilimin na’urar kwamfuta domin bunkasa harkokin noma a jihar.
Daraktan ma’aikata na karamar hukumar Lafia, Osabo Mohammed Ahmed ne ya yi wannan kalubalen a lokacin da yake bude taron horaswa na yini uku ga manoma wanda ya gudana a sakatariyar karamar hukumar Lafia.
Mohammed ya bayyana cewa duniya ta koma tamkar kauye guda, don haka akwai bukatar manoma su rungumi tsarin gudanar daharkokinsu a zamanance.
Da yake tabbattar da goyon bayan karamar hukumarsa ga shirin horaswar, Ahmed ya bayyana cewa noma mabudi ne na cigaba ga kowace al’umma.
Tun farko, babban manajan kamfanin kasuwancin kayan gona Steben Maduokor, ya ce dalilin bada horon shi ne don ilmantar da manoma kan harkar kasuwanci ta dandalin intanet.
Daga nan, ya yaba wa babbar bankin kasa da bankin manoma, ma’aikatar gona ta tarraya da sauran masu ruwa da tsaki kan mara wa hakar noma baya.
Maduokor ya bayyana cewa shirin horaswar zai taima wa manoma da ilimin inganta shuki da girbi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa yayin taron, wakilin babban banki kasa, Ogidi Akim ya sanar cewa babban banki kasa na da shirye-shirye masu yawa don amfanin manoma. Sannan ya gargadi jama’a kan bada cin-hanci ga wani kafin kai ga samun tallafin kudi daga babban bankin, tare da jaddada cewa bankin ba ya karbar ko sisin kwabo kafin tallafa wa shiri.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da manema labarai, sun nuna godiyarsu ga wadanda suka shirya taron, tare da bada tabbacin cewa za su yi amfani da irin darussan da suka koya.