Yasir Ramadan Gwale" />

Kalubalen Da Ke Gaban Masu Zave A 2019

 

A ranar 19 ga watan nan, wata jarida a Najeriya ta yi wani bincike kan ‘yan majalisun dokoki na tarayya inda ta yi bayanin irin kudaden da suka karva da kuma bayanin wadan da suka je majalisa suka yi zaman dumama benci, ba tare da sun yi ko da kwakkwaran tari ba, domin gabatarwa a matsayin kuduri ko wata doka da suke jin ta shafi al’ummar da suke wakilta.

Jaridar ta bayyana sunayen ‘yan majalisa 161 a cikin su 360, wanda babu abinda suka yi a zamansu na ‘yan majalisa sai zama kawai suna karvar albashi da alawus alawus, suna yawon duniya da sayen manyan motoci na alfarma da gina gidaje na kece raini da sauransu.

Jaridar ta bayyana cewar ‘yan majalisar sun lakume zunzurutun kudi har Naira biliyan 32, haka kuma, wadannan ‘yan majalisa kowannensu yana samun Naira miliyan 7.6 amatsayin alawus na tafiyar da ofis dinsa duk watan duniya! Sannan kuma suna karvar albashin 660,000 duk watan duniya, idan ka jimlace kudaden kowanne dan majalisa yana samun Naira miliyan 8.26 a duk watan duniya, yayi aiki ko bai yi ba.

Jaridar ta bayyana cewar a cikin ‘yan majalisar guda 161 da suka yi zaman dumama kujera a majalisar galibinsu wadan da suka fito daga yankin Arewa maso Yamma ne, inda ake da ‘yan majalisa 91, a cikinsu kuwa kusan kashi 60 zamansu kawai suke babu abinda suke sai dais u kalli zaman majalisa idan ma suna zuwa zauren majalisar.

Jaridar ta bayyana cewar a cikin wadan da suke zaman dumama kujera a majalisar hard a Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne babban mai tsawatarwa na majalisa, kuma Shugaban ‘yan majalisa 91 da suka fito daga yankin Arewa maso yamma, tun zuwansa majalisa a 2015, babu wani abu da yayi na bayar da kyakkyawan wakilci.

To ko shakka babu wannan abu da ban takaici yake, domin an tura mutanan das am sam sam bas u ma san aikin da aka tura su zuwa majalisa su yi ba, sun buge da yawon tazubar a Abuja, suna sayan manyan motoci da gidaje da kwana a dakunan otal masu tsadar tsiya, ba tare da sun yiwa al’ummar da ta zave su wakilci na gari ba.

Wannan babban laifi ne da ‘yan majalisar suka tafka, wanda sam bai kamata a sake basu damar komawa majalisa ba a zaven 2019 dake tafe. Idan an bi ta barawo a bi ta mabiyinsa, a zaven da ya gabata an sha gayawa mutane das u zabi cancanta ba jam’iyya ba, amma da yawa suka yi kunnen uwar shegu, suka rika zaton a yi sak a zabi duk wanda yake jam’iyyar Shugaban kasa komai lalacewarsa, kuma abin mamaki wadan da aka ce a zave su dan su taimakawa Shugaban kasar su ne suka fara kiran da a tsige Shugaban kasar daga majalisar wakilai.

Wannan wani babban kalubale ne da dole a wayar da kan jama’a das u fahimci meye aikin dan majalisa, sannan su san way a kamata su zaba, ina amfanin mutum ya tara jama’a yana raba musu kudade da injin markade da Babura da wayoyin hannu, a matsayinsa na dan majalisa amma babu abinda yake yi sai dumama kujera, bai ma san aikin da aka tura shi Abuja yayi ba, illa kawai dai yaga ana bashi albashi da alawus duk wata ga katon ofis da ma’aikata.

A wannan zave na 2019 akwai kalubale da yawa a gaban talakawa, Talakawa ina nufin masu zave, ya zama tilas mu dawo daga tunanin inna rududu, wato kawai a yi Sak, duk jam’iyyar da ake son wani jagoranta kawai mitane su zabi duk wanda jam’iyyar ta tsayar ba tare da duba cancantarsa da dacewarsa ba, tilas mutane su ji tsoron Allah su tsaya su duba wadan da suka tsaya zave su duba su tace suga way a kamata su zaba domin basu kyakkyawan wakilci.

Haka kuma, akwai aiki ja a gaban kungiyoyin sa-kai na al’umma das u tashi tsaye wajen wayar da kan mutane kan sanin hakikanin wanda ya dace a zaba a kowanne irin mataki na zave, a yi wannan kuma tsakani da Allah ba tare da son rai ko karkata zuwa ga wani bangare ba, wajibinmu ne mu tsayi mu yi karatun ta nutsu gaba dayaa, mu gano kusakuranmu mu kuma nemi sahihan hanyoyin kawo gyara domin kyautatuwar gobenmu da kuma goben ‘yan bayanmu.

Wani abin ban haushi da takaici, shi ne, yadda irin wadannan mutane da babu abinda suka iya tsinanawa al’umma a mukamai ko matakan da suka taka, sune kuma galibi suke son maye gurbin mukaman da suke kai da ‘ya ‘yansu, mutum yayi mukami ya gaji bai yiwa al’umma wani abin kuzo mu gani ba, amma kuma yana son dansa na cikinsa ya gaje shi a matsayin wanda zai cigaba da jan ragamar tunanin al’umma, kai kace shi gadar abin yayi daga mahaifinsa.

Lallai ya kamata mu fadaku mu san abin yi tun kafinlokaci yaa kure mana, wadannan mutane 161 da muka tura majalisa da nufin bamu wakilci na gari, babu abinda suka yi mana illa cusa mana haushi ta hanyar zaman dumama benci ba tare da sun amfana mana komai ba, dan haka kada a yaudari mutane da rabon kayan tallafi da galibin ‘yan majalisu suke yi, idan azumi yazo su raba shinkafa, in Sallah ta zo su raba shadda, sannan su raba injin ban ruwa da injin markade da taliya da sauransu.

Yana da kyau jama’a su sani ba wannan ne aka zave su dominsa ba, an zave su ne domin kare muradun al’ummarsu da kuma bayar da kyakkyawan wakilci ga al’umma tare da gabatarwa da majalisar kasa koke ko halin da al’ummarsu suke ciki, duk mutumin da ya kasa yin wannan duk abinda zai rabawa mutane na kyautatawa mutane su karva amma idan zave ya zo kada su zave shi, su zabi wanda zai kare mutuncinsu da addininsu da al’umma ko da kuwa bai bayar da komai ba.

Idan muka yi sake irin wadancan ‘yan majalisa 161 da suka yi zaman banza a majalisa suka dawo da jakar kudi suna rabawa domin sake zavensu, to mu sani zasu sake yin wasu Karin shekaru 4 ne suna zaman banza ba tare da bayar da kyakyawan wakilci da jagoranci na gari ba, dole mu yadda da halin da muke ciki mu kuma jajirce mu yaki talaucin zuci wanda shi ne yake mana illa, dan abu kalilan  da bai taka kara ya karya ba sai ya karya mana guiwa mu rika zaven mutanan dab a su cancanta ba, kawai saboda sun mallaki abin duniya sai mu rika binsu inna rududu, su kuma babu abinda ya damesu sai kansu da iyalansu, su kashe ‘ya ‘yansu su kai kasashen waje su yi karatu, bayan sun kasa bayar da wakilcin da za’a gyara harkar ilimi a Najeriya domin danka da dana.

Irin wadannan ne fad a suka kasa gyara mana harkar ilimi a kasarnan suka yi shakulataun bangaro da batunsa, suke fatan ‘ya ‘yansu zasu gaje su a kowanne irin matsayi, sun jahltar da namu yaran ta hanyar yin wasarairai da harkar ilimi, suka kwashe nasu suka kai inda suka samu ingantacce ilimi, sannan nan gaba idan sun tsufa sais u turo yaransu su dora daga inda ya tsaya.

Kamar yadda na fada, kada a yaudaremu dad an abinda ba zai amfana mana komai ba, su yi ta mana dariya in suna tare da mu, amma basa sonmu basa kaunarmu, duk wata dama in tazo abinda zasu fara yi shi ne tunanin ‘ya ‘yansu, ba tunanin al’ummarsu ba, kaga yaransu bata taba yin aikin komai ba, amma sun yi kudi na fitar hankali, suna hawa zunduma zunduman motoci suna yiwa al’umma girman kai da nuna isa, da tunain dole ne a bisu tunda iyayansu sun yi wani abu a zatonsu.

Bugu da kari, zaka ga wasu mutanan saboda mutuwar zuciya,suna yiwa mutum da’a da biyayya ta karya domin su samu wani abu a wajensa, sannan kuma su koma suna yiwa dansa dan shima ya basu wani abu, mutum yayi Sanata ko Gwamna ko wani babban mukami babu abinda ya tsinanawa al’umma sai muguwar sata da ya tafka, ya azurta kansa da ‘ya ‘yansa, sannan kuma mutane su rika binsa kuma suna bin ‘ya ‘yansa domin samun abin batarwa.

Allah ya sa mu gane kuma mu fadaku. Lallai mu sani a zaven 2019 mu jajirce wajen zaven mutane na gari, wadan da suka dacezasu iya taimakon al’umma, zasu iya bayar  da kyakkyawan wakilci ko a wacce jam’iyyar suka fito, tunanin da wasu suke yin a cewar sub a zasu taba zaven wata jam’iyya ba duk kirkin mutanan cikinta, wannan ra’ayin rikau ne marar amfani, ba addini bane balle ace ba za’a daina ba ko ba za’a yi ba. Allah yasa mu gyara.

 

 

Exit mobile version