Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsala da kalubalen masu bayan-gida a bainar jama’a ke haifarwa, a halin yanzu kididdiga ya nuna cewa, fiye da al’ummar Nijeriya Miliyan 48 ke ci gaba da wannan mummunan dabi’ar.
Rahoton kungiyar gidauniyar majalisar dinkin duniya mai kula da yara UNICEF ta bayyana cewa, Nijeriya na a kan gaba a cikin kasashen duniya da aka fi yin ba-haya (Kashi)a bainar jama’a.
- Kasar Sin: Ya Kamata A Martaba Mabambantan Addinai
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Fitar Da Takin Zamani Da Hatsi Don Rage Radadin Cire Tallafin Fetur
Rahoton ya kuma bayyana cewa, kusan kashi 46 na al’ummar Nijeriya, fiye da mutum miliyan 90 ke nan ba su da cikakken makewayi inda ya zame musu tilas su shiga yin bayan-gida a bainar jama’a tunda ba su da wani zabi.
Shugabar hukumar kula da tsarin samar da ruwa da tsaftace muhalli karkashin UNICEF, Jane Beban, ta jaddda rashin issasun dakunan ba-haya a kasar nan inda ake bukatar samun gina akalla gidan ba-haya 180,000 zuwa 200,000 a kowanne shekara.
UNICEF ta bayyana cewa, Nijeriya na bukatar gina akalla gidan ba-haya miliyan 20 a gidajen al’umma a kuma kwai bukatar gina ba-haya miliyan 43,000 a makarantunmu da cibiyoyin kula da kiwon lafiya in har ana son Nijeriya ta samu nasarar kawar da ba-haya a bainar jama’a nan da shekarar 2025.
Misis Beban ta kuma bayyana muhimmancin a samar da gidan gidajen ba-haya a sassan kasa don kawo karshen yadda al’umma ke ba-haya a bainar jama’a a Nijeriya.
Haka kuma masana da masu ruwa da tsaki sun bayar da shawarar cewa, akwai bukatar gwamnatin Nijeriya ta zuba jarin da ya kai fiye da Naira Tiriliyan 1.9 don yin maganin matsalolin da suka shafi samar da tsaftataccen ruwa, tsaftace muhalli da kuma kawar da matsalolin da suka shafi yin ba-haya a bainar jama’a nan da zuwa shekarar 2025.
Wannan kudin da ake bukata ya zarce naira Miliyan 10 da gwamnatin tarayya ta ware tun da farko da aka kaddamar da shirin a shekarar 2016. A shekarar 2019, gwamnatin tarayya ta kaddamar da dokar ta baci tare da kaddamar da tsarin kawar da bayan-gida a bainar jama’a daga nan zuwa shekarar 2025.
Amma kuma binciken da aka yin a baya-baya nan ya nuna cewa, Nijeriya na tafiyar hawainiya a wannan fannin kuma ba a samu nasarar da ya kamata ba a kokarin kawar da yin ba-haya a bainar jama’a a Nijeriya.
A tattaunawar ta da wannan jaridar, Darakta a ma’aikatar albarkatun ruwa, Chizoma Okpara, ta sanar da cewa a halin yanzu, kananan hukumomi 102 a jihohi 14 daga cikin jihohi 36 na tarayyar kasar nan suka cimma kudurin kawar da ba-haya a bainar jama’a a tarayyar kasar nan.
Ta kuma kara da cewa, Jihar Jigawa da ke yankin arewa maso yammacin Nijeriya ta samu nasarar zama jihar da ba a ba-haya a bainar jama’a a cikinta yayin kuma jihohin Anambra, Akwa Ibom, Bauchi, Benue, Borno, Cross Riber, Kano, Kaduna, Katsina, Osun, Yobe, da Zamfara suma suka kai matsayin kawo karshen yin ba-haya a bainar jama’a.
Abin takaici kuma shi ne jihohin da suka fi yawan al’umma kuma Kano da jihohin da ke a kan gaba a bangaren kasuwanci, kamar jihar Legas, Ribas, Kross Ribas suna fama da al’umma da dama masu ba-haya a bainar jama’a.
Lamba na 6.2 na dokokin muradun karni (SDGs) ya umarci ganin a kawo karshen yi ba-haya a bainar jama’a da kuma ba al’umma damar samun cikakken tsaffataccen muhalli musamman ga mata da kananan yara wadanda suka fi jin radadin matsalar tattalin arziki da kuma matsalolin da al’adu ke haifarwa ga rayuwar al’umma.
Masana harkokin kiwon lafiya sun bayyana cewa, yara fiye 90,000 ke mutuwa sakamakon cututtukan da suka shafi tsaffatace muhalli. Shirin kawo karshen ba-haya a bainar jama’a wata dama ce na kawo karshen wadannan mace-macen.
Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, yin ba-haya a bainar jama’a na nufin cewa, yin kashi a wani wuri ba a nan aka shirya yi ba. Wasu na iya zaban yin ba-hayan a fili, daji, rami ko kuma a cikin kogi saboda rashin wuraren yin ba-haya ko kuma rashin inda aka shirya yin ba-hayan.
A yayin bikin ranar ba-haya ta duniya da aka yi a shekarar 2021, tsohon ministan albarkatun ruwa, Suleiman Hussein Adamu, ya lura a cewa, yin ba-haya a bainar jama’a na tattare da yiwuwar haifar da cuttutuka da suka shafi rashin tsafta, rashin ilimi da talauci, hakan kuma yana shafar martabar al’umma da kuma kariya ga mata da ‘yan mata a yayin da suka shiga daji don yin ba-haya.
Da yake kawo kididdiga daga rahoton bankin duniya na shekarar 2021, tsohon ministan ya bayyana cewa, Nijeriya na asarar fiye da Naira biliyan 455 daidai da Dala Biliyan 3 sakamakon rashin tsaftace muhalli a kowacce shekara.
A ra’ayin wannan jaridar, musamman ganin yadda ake gangamin yekuwar ganin bayan yin kashi a bainar jama’a a Nijeriya, yana da matukar wahala a iya kawo karshen wannan lamarin daga nan zuwa shekarar 2030 kamar yadda tsarin muradun karni na majalisar dinkin duniya ya tanada.
Idan aka lura da cewa, kananan hukumomi 102 ne kawai suka kai matsayin kammala yaki da yin kashi a bainar jama’a a cikin kananan hukumomi 774 da muke da su a fradin tarayyar kasar nan.
Yayin da jiohohi da dama ke kokkarin sun cimma wannan matsayi, wasu jihohi kamar jihar Kross Ribas ba su yi niyyar ganin sun kai ga wannan matsayin ba.
Rashin jajircewar gwamnoni na daya daga cikin manyan matsalolin da shirin yaki da kashi a bainar jama’a ke fuskanta.
Muna yabo da jinjina ga majalisar kasa ta 10, inda suka nemi ‘yan majalisar su sanya shirin samar da dakunan ba-haya a cikin kasafin kudi na yankunansu, muna kuma fatan lamarin zai wuce hakan don a samu nasarar da ake bukata na fatattakar yin ba-haya a bainar jama’a a fadin Nijeriya.