Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaban APC ne a yayin zaman kwamitin zartarwa na jam’iyyar karo na 12 da ya gudana a Abuja.
Kwamitin zantarwa ya kasance shi ne na biyu mafi girma wajen yanke hukunci a jam’iyyar APC kuma mambobinsa sun hada da shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnonin APC wadanda suka kasance mambobi a kwamitin gudanarwa da shugabannin jam’iyyar na jihohi da dai sauransu.
An dai zabi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar bayan murabis din tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu wanda ya fito daga yankin arewa ta tsakiya.
Ganduje ya kasance shugaban APC na shida bayan shudewar mulkin shugabanin da suka jagoranci jam’iyyar, Cif Bisi Akande daga 2013 zuwa 2014, Cif John Odigie-Oyegun daga 2014 zuwa 2018, Kwamard Adams Oshiomhole daga 2018 zuwa 2020). Mai Mala Buni daga 2020 zuwa 2022 da kuma Sanata Abdullahi Adamu daga 2022 zuwa 2023.
Wannan shi ne karon farko da wani shugaban jam’iyyar na kasa ban da mai rikon kwarya ya zama shugaban jam’iyyar bayan ganawar kwamitin zartarwa tun bayan kafa ta a shekarar 2013.
Idan za a tuna, wakilai ne suka zabi tsofaffin gwamnonin Jihar Edo, Oshiomhole da Odigie-Oyegun, da kuma Sanata Adamu wadanda suka kasance jiga-jigan shugabannin jam’iyyar na kasa a babban taron da jam’iyyar ta gudanar.
An zabi Odigie-Oyegun a babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar a watan Yunin 2014, shi kuwa Oshiomhole ya zama shugaban jam’iyyar ne a taron da aka gudanar a watan Yunin 2018, yayin da Adamu ya zama shugaban jam’iyyar a babban taron kasa da aka gudanar a dandalin Eagle Skuare a watan Maris 2022.
Buni ya zama shugaban riko na jam’iyyar APC a lokacin wani taro da zartarwa ta gudanar a watan Yunin 2020, amma bai kasance zababben shugaban jam’iyyar kasa ba. An bai wa kwamitin Buni wa’adin lokacin da zai shirya babban taron kasa don zaben sabbin shugabannin APC.
Cif Akande wanda ya zama shugaban rikon kwarya a yayin taron jiga-jigan jam’iyyar a matsayin wani bangare na ka’idojin rajistar jam’iyyar kuma ya mika ragamar shugabancin jam’iyyar ga Odigie-Oyegun a lokacin da aka zabe shi a babban taron jam’iyyar a shekarar 2014.
Sai dai lamarin Ganduje ya bambanta, domin ya maye gurbin Adamu ne, wanda ya fito daga yankin arewa maso yamma a yayin taron kwamitin zartarwa ba ta hanyar zaben wakilai ba a lokacin babban taro na kasa.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa lamarin ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2022.
Ita dai kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya dagara ne da sahi na 13:3 (ii) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya sa Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar.
Amma babban abun tambayar shi ne, ko Ganduje zai iya hada kan ‘ya’yan da kuma samun goyon bayan jiga-jigan jam’iyyar APC, musamman daga shiyyar arewa ta tsakiya da sauran shiyyoyin domin ya samu nasara, ko kuma zai bi samun wadanda suka gabace shi wadanda suka bar mukamin tun kafin wa’adinsu ya kare.?
Wannan shi ne tambayoyi da masu sharhi suke yi, musamman yadda yankin arewa ta tsakiya ke ganin cewa an dakile su, inda suke cewa ya kamata yankin ya ci gaba da rike mukamin bisa la’akari da cewa wa’adin Adamu bai kare ba an tilasta masa yin murabus ne.
To sai dai kuma akwai ayar tambaya kan ko sabon shugaban jam’iyyar zai iya magance rudanin da ke cikin jam’iyyar ya mayar da ita kan tafarkinta ko kuma shi ma zai barta ta ci gaba da tafiya yadda aka saba.
Masu fashin baki sun bayyana cewa a halin yanzu dai jam’iyyar babu hadin kai saboda rikice-rikicen da ke faruwa da kuma yadda Ganduje ya samu zama shugaban jam’iyyar.
Idan za a iya tunawa dai, mashawarcin jam’iyyar kan harkokin shari’a, Ahmed El-Marzuk, ya yi murabus daga kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Ya yi murabus ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman, Abdul Halim Adamu, inda ya ce ba zai iya aiki da Ganduje ba.
Duk da cewa akwai alamun ana zarginsa da rashin gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da jam’iyyar, El-Marzuk ya yi murabus ne lokacin da Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar.
Haka zalika, mataimakin shugaban jam’iyyar reshen arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman ya yi murabus bayan ya nuna adawa da shirin maye gurbin Adamu da Ganduje, inda ya dage cewa arewa ta tsakiya ta ci gaba da rike mukaminta.
…Zan Sake Gyara APC –Ganduje
A jawabinsa na karbar ragamar shugabancin jam’iyyar, Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta sake gyara jam’iyyar da inganta dimokuradiyyar cikin gida da hadin kai da kuma kara yawan kujerun zartarwa da na majalisar dokoki da jam’iyyar ke da su a halin yanzu.
Gwamna Ganduje ya ce shugabancinsa zai samar da jagoranci mai kyau ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da ke takarar mukaman siyasa daban-daban a kasar nan. Ya jaddada cewa zabukan fid da gwani a jam’iyyar za su kasance cikin gaskiya da sahihance a karkashin kulawarsa.
Ya ce, “A karkashin kulawata, za a bi tsarin dimokuradiyyar cikin gida tare da tuntubar juna da kuma tabbatar da jam’iyyar ta yi aiki kafada da kafada da dukkan ‘ya’yanta.
“Dukkanmu mun amince cewa dole ne mu hada kan ‘ya’yan jam’iyyar domin samun goyon baya ga gwamnatinmu da kuma tabbatar da tunkarar kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a kullum.”