Hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC) ta kaddamar da horas da malamai 1,480 da aka zabo daga makarantun karkara a jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja.
Horon wanda zai mayar da hankali kan hanyoyin koyarwa na zamani, an zabo malamai 40 ne daga kowace jiha, a wani bangare na kokarin shawo kalubalen da ya dabaibaye bangaren koyarwa a kasar.
- Makarantar Horas Da ‘Yan Kwallo Ta Katsina Zata Wakilci Nijeriya A Gasar Kofin Dana Na Denmark
- Shettima Zai Je Amurka Don Halartar Taron Kasuwanci Tsakanin Amurka Da Afirka Na 2024
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar a Abuja ranar Litinin, Babban Sakataren Hukumar UBEC, Dakta Hamid Bobboyi, ya ce, daya daga cikin kalubalen da ke kawo cikas ga aiwatar da tsare-tsaren UBE a Nijeriya shi ne, gazawar shirin zuwa ga wasu dalibai da ke can cikin kauyuka masu nisa.
Shugaban UBEC wanda mataimakin babban sakataren hukumar Farfesa Bala Zakari ya wakilta ya ce, hukumar ta bullo da shirin karawa malaman sabuwar hikimar koyarwar zamani ne domin baiwa daliban ingantaccen ilimi.