Khalid Idris Doya" />

Kamaru Za Ta Raba Gidan Sauro Miliyan 15 Kyauta

A shekaranjiya Alhamis gwamnatin kasar Kamaru ta kaddamar da aikin fara rabon gidajen sauro miliyan 15 kyauta a duk fadin kasar domin rage matsalar yaduwar kwayar cutar zazzabin cizon sauro.

“Muna burin kammala yankunan da matsalar ta fi kamari. A lokacin da muka shirya gangamin fadawar da al’umma kan muhimmancin amfani da gidajen sauro, muna sa ran za’a samu raguwar adadin mutanen dake kamuwa da cutar malariyar da wadanda ke mutuwa a sanadiyyar cutar da kashi 50 bisa 100,” ministan kula da lafiyar al’umma na kasar Kamaru, Manaouda Malachie, shi ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da shirin a shiyyar gabashin kasar.

A cewar ministan, Jamhuriyar Kamaru ta samu matukar raguwar adadin mace-macen da ake samu a sanadiyyar cutar maleriya a cikin shekaru 7 da suka gabata.

Adadin ya ragu daga kaso 33 bisa 100 a shekarar 2011 zuwa kaso 24 bisa 100 a shekarar 2018 sakamakon yadda ake samun karin wayar da kan al’umma, da yin rigakafi da kuma warkar da wadanda suka kamu da cutar, a cewar Sinata Koulla-Shiro, babbar sakatariyar ma’aikatar kula da lafiyar al’umma ta Kamaru.

“Wasu daga cikin dalilan da suka taimaka wajen raguwar matsalar sun hada da bayar da gidajen sauron kyauta ga mata masu juna biyu, da bayar da magunguna kyauta ga yara ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa, kana da kuma saukaka farashin magunguna ga sauran jama’a dake fama da cutar maleriyar,” in ji Koulla-Shiro.

Exit mobile version