Kamfanin Dangote ya sanar da shiga da kuma ɗaukar nauyin Bikin Bajekoli na jihar Kano (Kano International Trade Fair) da za a gudanar daga 22 ga Nuwamba zuwa 6 ga Disamba, 2025. Shugaban sashin hulɗa da jama’a na kamfanin, Anthony Chiejina, ya bayyana cewa an shirya samun fiye da kamfanoni 1,000 daga cikin gida da ƙasashen waje a bana.
Chiejina ya ce Kano na da mahimmanci ga harkokin kamfanin saboda matsayinta na cibiyar kasuwanci a Nijeriya da ma nahiyar Afrika. Ya ƙara da cewa kamfanin na gina wani katafaren babban injin sarrafa shinkafa a Kano tare da wasu injinan niƙa a Jigawa, da Zamfara, da Niger, da Kebbi da kuma Sokoto da za su samar da tan miliyan 1.5 a duk shekara, domin tallafa wa gwamnatin tarayya a ƙoƙarinta na cimma bunƙasar abinci.
- ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote
- Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote
A cewarsa, sassan kamfanin Dangote za su samu manyan rumfuna na musamman a filin bajekoli domin karɓar tambayoyi da tattaunawa kan haɗin gwuiwa. Haka kuma, kamfanin zai ƙaddamar da sabbin nau’ikan buhunan sikari masu girman 100g da 25kg.
Mashawarcin Shugaban Kamfanin Dangote kan aiyukan musamman, Fatima Wali-Abdurrahman, ta ce shiga bikin Bajekolin na bana wani yunƙuri ne na ƙarfafawa ƙananan masana’antu da samar masu damar faɗaɗa kasuwa, da samun abokan hulɗar kasuwanci da kuma samar da sabbin hanyoyin tattalin arziƙi.
Shugaban KACCIMA, Ambasada Hassan Usman Darma, ya shaida wa manema labarai cewa ana sa ran kamfanoni kusan 100 da masu baje koli sama da 1,000 za su halarta. Ya ce an inganta wajen Bajekolin sosai a bana.














