Kamfanin kula da albarkatun mai ta Nijeriya (NNPCL) ya rage farashin litar mai a gidajen mai da suke Abuja daga naira 1,030 zuwa N965.
Wannan dai shi ne rage farashin litar mai sau biyu cikin makwa biyu da kamfanin mai na kasar ya yi biyo bayan ragi da ya yi daga naira 1,060 zuwa naira 1,030 na kowace lita domin gogayya da matatar man Dangote.
- An Roki Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Tallafi Ga Aikin Hajjin 2025
- Ƙasa Da Sa’o’i 30 Da Rasuwar Mahaifiyarsa, Gwamnan Jigawa Ya Sake Rasa ÆŠansa A Hatsarin MotaÂ
Matuka ababen hawa da dama sun yi maraba da wannan matakin, inda ‘yan jarida suka zaga gidajen mai da ke Abuja domin tabbatar da aiwatar da ragin.
Wani direban motar kabu-kabu da ke kasuwancinsa a Nyanya zuwa Zuba ya lura da ragin a matsayin mataki mai kyau, ya kuma sake yin kira da a sake samun karin ragin litar na mai, inda ba da shawarar a samu karin ragin zuwa naira 530 kan kowace lita.
Kazalika, wani direban mota mai zaman kansa, ya nuna jin dadinsa da matakin, inda ya misalta hakan da yunkurin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na farfado da tattalin arziki.
Ya tabbatar da cewa ragin zai yi matukar kyautata yanayin tattalin arziki da rage wa jama’a matsin rayuwa da ake ciki.