Sanusi Chen" />

Kamfanonin Amurka Sun Yi Watsi Da Zargin ‘Bloomberg Businessweek’ Kan Kasar Sin

A kwanan baya, Mujallar Bloomberg Businessweek ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, kasar Sin ta sanya wata karamar na’urar lantarki cikin kayayyakin da kamfanonin Amurka kimanin 30 suka kera domin neman bayanan sirri. Amma kamfanonin da abin shafa kamar su Apple Computer Inc. da Amazon.com Inc. sun bayar da sanarwoyi, inda suka musunta labarin tare da bayyana shi a matsayin maras tushe.

A cikin sanarwar da kamfanin Apple Computer Inc. ya bayar, ya ce a cikin shekara guda da ta gabata, Mujallar Bloomberg Businessweek ta sha ba da labarin cewa, akwai matsalar tsaro a kamfanin, amma kamfanin bai taba ganin irin wannan mummunar na’urar lantarki ba, kuma bai taba tuntubar hukumar bincike ta tarayyar kasar Amurka wato FBI da sauran hukumomin tafiyar da dokokin kasar ba kan wannan batun. Bugu da kari kamfanin Apple Computer Inc. ya mika wasika ga majalisar dokokin Amurka domin sake ba da sanarwar rashin samun kowace shaida da ke da nasaba da labarin mujallar.

A nasa bangaren kuma, kamfanin Amazon.com Inc. ya ba da sanarwar cewa, labarin da Bloomberg Businessweek ya bayar ba gaskiya ba ne. Kamfanin ya ce bai taba gano matsala ko daya da ke da nasaba da batun sanya karamar na’urar lantarki ba, kuma bai taba hadin kai da gwamnati wajen binciken batun ba. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, akwai kura-kurai masu dimbin yawa da aka bayar kan kamfanin Amazon.com Inc. a cikin labarin.

Bisa labarin da Mujallar Bloomberg Businessweek ta bayar, an ce, kasar Sin ta sanya kamarar na’urar lantarki mai satar bayanai ta Intanat cikin kayayyakin kamfanin Super Micro. Game da wannan, kamfanin ya ba da sanarwar cewa, bai taba gano wata mummunar na’urar ba. Kana hukumomin tafiyar da doka na Amurka ba su taba yi masa bincike ba.

Bugu da kari, kamfanonin AT&T, Sprint Corp, Verizon su ma sun ba da sanarwa, inda suka musunta ganin na’urorin lantarki da ke cikin tsare-tsaren tunanin manhajarsu. Hukumar tsaron kasar Amurka ta kuma furta a watan da muke ciki cewar, babu dalilin shakku kan sanarwoyin da kamfanonin Amurka suka bayar kan labarin da Bloomberg Businessweek ya bayar.  (Mai Fassarawa: Kande Gao, ma’aikaciyar sashen Hausa ta CRI)

 

Exit mobile version