Kimanin wata bakwai da suka gabata, na rubuta sharhi mai taken “Ya Dace Nijeriya Ta Bi Sawun Kasashe Masu Shirin Fita Daga Kangin Dalar Amurka”. Na kawo misalai da kasashe irin su Argentina, Brazil da Bolivia da suka fara amfani da kudin kasar Sin, Renminbi a kasuwancin dake tsakaninsu da Sin da kuma yadda lamarin yake kara samun karbuwa a yankin Latin Amurka da Caribbean.
A wancan lokacin, na yi hasashen Dala 1 na iya zarta Naira 1,000, kuma tabbas hasashe nawa ya zama gaskiya, domin yanzu haka farashin gwamnati na kwan-gaba-kwan-baya ne a tsakanin 1,500 kowace dala.
A sakamakon haka, ‘yan Nijeriya na fuskantar daya daga cikin mafi munin tabarbarewar tattalin arziki da ba a ga irinsa ba cikin shekaru da dama sakamakon hauhawar farashin kayayyaki sanadiyyar kangin Dalar Amurka.
Alkaluman gwamnati na baya-bayan nan da aka fitar, sun nuna hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairu ya karu zuwa kashi 29.9%, mafi girma tun daga shekarar 1996. Darajar kudinmu ta karye da kashi 230% a kasa da shekara guda kacal!
Wannan abu ya tsaya mana a kahon zuci. Ya kamata a hanzarta lalubo bakin zaren magance lamarin. Tun da tattalin arzikinmu galibi ya fi dogara ne kan shigo da kaya daga kasashen waje, ya dace a mayar da hankali wajen habaka kasuwanci da kasashen da za mu iya hulda da su ba tare da Dalar Amurka ba.
Wannan lokaci zai zama mafi dacewa na farfado da yarjejeniyar musanyar kudi a tsakanin Nijeriya da Sin wanda aka so yi a shekarar 2018, ta kimanin Naira Biliyan 720 kwatankwacin RMB Biliyan 15 (a wancan lokaci), amma wasu suka yi wa abin kafar ungulu.
Tabbas idan aka yi haka, zai rage mana radadin kangin dala, domin zuwa watan Nuwambar 2023, kasuwancin dake tsakanin Sin da Nijeriya ya kai na Dala Biliyan 22.6 (sama da Naira Tiriliyan 35). Kuma ana sa ran wannan ya karu saboda yadda kasar Sin ta fi kowacce huldar kasuwanci da kasashen waje a duniya, sannan Najeriya ita ce ta uku a yawan kasuwancin da Sin ke yi da Afirka.
Kamar yadda Karamar Jakadiyar kasar Sin a Nijeriya Yan Yuqing, ta bayyana a kwanan baya, “A shekarun baya-bayan nan, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya a fannonin filin jirgin sama, tashar jiragen ruwa, layin dogo, hanyoyin mota, hanyoyin sadarwa da sauran ababen more rayuwa sun samu babbar nasara. ” Ta bayyana hakan ne a Legas a wajen bikin lale marhabin da isowar jirgin ruwa na CMA CGM Scandola, wanda ya kasance mafi girman dakon kwantena da ya ziyarci tashar ruwan Nijeriya a bana zuwa yanzu.
Sabo da siyasar duniya, Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta ci gaba da tilasta wa Nijeriya amfani da Dalarta a kasuwancin kasashen waje, amma kuma mai daki shi ya san wurin da yake masa yoyo, kangin da Dalar ta jefa mu ya yi yawa, me ya sa za mu ci gaba da kashe kanmu don kawai wata kasa ta ci gaba da jan zarenta a duniya?
A wani littafinsa na baya-bayan nan, “Edible Economics: A Hungry Economist Explains the World”, masanin tattalin arziki dan asalin Koriya ta Kudu na Jami’ar London, Ha-Joon Chang, ya yi tsokacin cewa, “Duk da kasashen Afirka sun sha wahala fiye da yadda kasashen Latin Amurka suka sha daga manufofin yarjejeniyar Washington (wacce John Williamson ya gabatar a 1989), amma kuma sun gaza fitowa baro-baro a fili su yi watsi da su (manufofin), ganin yadda suka fi dogaro da cibiyoyin Washington don samun kudade. Amma kuma, a cikin shekaru goma da suka wuce, ana samun karuwar amincewa da bukatar lallai kasa ta yi wa kanta kiyamullaili fiye da abin da Yarjejeniyar Washington ta ba da shawara a kai.”
Akwai kasashe da suka samar wa kansu mafita, misali, Rasha da Sin suna cinikayya ta amfani da kudinsu Yuan da Rubles maimakon Dalar Amurka. Haka nan masu sayen man Rasha a Indiya suna biyan galibin kudin ne da ko dai kudin Rashar ko kuma Dirham na Hadaddiyar Daular Larabawa. Ko a nan Afirka ma, Kenya ta kulla yarjejeniya da Kamfanin Mai na Saudiyya (Aramco) da na Abu Dhabi (Adnoc) da za su rika shigo mata da fetur da gas, ita kuma tana biya da kudin kasarta na Shillings. Don haka, ya kamata Nijeriya ta bi sawu.