Gwamnatin Jihar Ribas ta dakatar da duk masu riƙe da Muƙaman siyasa a faɗin jihar daga aiki nan take.
Wannan mataki na cikin wata sanarwa da Kantoman Ribad, Manjo Janar Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya fitar a daren ranar Laraba.
- Wang Yi Ya Gana Da Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasa Na Amurka Mai Lura Da Alakar Sin Da Amurka
- Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A Nijar
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa ga ikon da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa Ibas.
Waɗanda abin ya shafa sun ha5da da Sakataren Gwamnatin Jihar, Shugaban Ma’aikata, dukkanin Kwamishinoni, tare da mambobin kwamitoci, hukumomi, da cibiyoyin gwamnati.
Haka kuma, dukkanin Masu Ba da Shawara na Musamman, Mataimaka na Musamman, su ma an dakatar da su.
Sanarwar ta umarci dukkanin waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga Sakatarorin ma’aikatun da suke jagoranta.
Idan babu Sakatare, sai miƙa ragamar ga babban Darakta mafi girma ko Shugaban Harkokin Gudanarwa.
Wannan umarni zai fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp