Wata ƴar karamar gobara ta tashi a yau Larabar a sashen kula da matatar man fetur ta Dangote. Hukumar kula da matatar man ta Dangote tabbatar da cewa an shawo kan gobarar da ta shi a matatar ba tare da bata lokaci ba, tare da bayyana gobarar a matsayin wata ƙaramar gobara.
Anthony Chiejina, mai magana da yawun kamfanin Dangote ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kwantar da hankulan jama’a tare da jaddada cewa babu wani abin fargaba.
- An Tona Asirin Masu Yi Wa Matatar Dangote Zangon Ƙasa
- Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa’adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta
Chiejina ya tabbatar da cewa an shawo kan gobarar cikin gaggawa kuma matatar ta ci gaba da aiki kamar yadda aka saba. Ya kuma ba da tabbacin cewa ba a samu rauni ko jikkata a tsakanin ma’aikatan da ke bakin aiki ba.