CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Kare Muradun Kasa Fiye Da Batun Rigakafin COVID-19 Na Barazana Ga Kokarin Da Kasashen Duniya Ke Yi Wajen Yaki Da Cutar

by CRI Hausa
July 14, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Kare Muradun Kasa Fiye Da Batun Rigakafin COVID-19 Na Barazana Ga Kokarin Da Kasashen Duniya Ke Yi Wajen Yaki Da Cutar
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ranar 12 ga wata, jaridar USA Today ta wallafa wani labari dake cewa, kasashen Amurka da Birtaniya da wasu kasashe ba su tsara da kuma aiwatar da tsare-tsaren duniya kan nazari da rarraba allurar rigakafin cutar annobar COVID-19 ba, inda suka kare muradun kasashensu kawai. Yadda suke kare muradun kasashensu fiye da batun rigakafin cutar yana barazana ga kokarin da kasashen duniya suke yi wajen yaki da cutar ta COVID-19. A don haka, ba za a samu lafiya a duniya ba, sai dai kowa ya yi kokarin samarwa kansa lafiya.

Haka zalika, jaridar Financial Times ta Birtaniya ta ba da labari a kwanan baya cewa, yanzu wasu kasashe, ciki had da Amurka da Birtaniya sun kare muradun kasa fiye da batun rigakafin cutar COVID-19. Inda suke goyon bayan nazarin allurar rigakafin cutar a kasashensu, yayin da suka bukaci a bai wa al’ummominsu allurar kafin sauran al’ummomin kasashen duniya.
Wasu masana lafiyar al’umma na duniya sun nuna damuwa cewa, yanzu babu wani tsari da aka bullo da shi game da yadda za a rarraba allurar tukuna, wanda ya samu amincewar sassa daban daban. David Fidler, babban manazarcin lafiyar al’ummar duniya a kwamitin kula da huldar jakadanci na Amurka ya bayyana ba tare da rufa-rufa ba cewa, da kyar a samu wani dan siyasa da zai ce, a fara bai wa kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara kaso 30 cikin 100 na allurar rigakafin cutar COVID-19. (Tasallah Yuan)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Birnin Rongcheng Na Lardin Shandong Na Ba Da Kulawa Sosai Ga Tsoffi

Next Post

Gibin Dake Tsakanin Masu Kudi Da Talakawa Ya Haifar Da Karuwar Matsalolin Da Suke Shafar Kare Hakkin Bil-Adama A Amurka

RelatedPosts

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Duba Marasa Lafiya Sama Da 4,000 A Ghana A 2020

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Duba Marasa Lafiya Sama Da 4,000 A Ghana A 2020

by CRI Hausa
1 hour ago
0

Tawagar jami’an lafiya ta kasar Sin kashi na 9 dake...

Amurka Ta Kasa Magance Matsalar Rashin Daidaito A Cikin Al’ummarta

Amurka Ta Kasa Magance Matsalar Rashin Daidaito A Cikin Al’ummarta

by CRI Hausa
2 hours ago
0

Sakamakon bazuwar cutar COVID-19, wadda ta raunana tattalin arzikin duniya...

Mike Pompeo Zai Kammala Aikinsa Na Ministan Harkokin Waje

Mike Pompeo Zai Kammala Aikinsa Na Ministan Harkokin Waje

by CRI Hausa
2 hours ago
0

A cikin kwanaki 10 da wani abu da suka gabata,...

Next Post
Gibin Dake Tsakanin Masu Kudi Da Talakawa Ya Haifar Da Karuwar Matsalolin Da Suke Shafar Kare Hakkin Bil-Adama A Amurka

Gibin Dake Tsakanin Masu Kudi Da Talakawa Ya Haifar Da Karuwar Matsalolin Da Suke Shafar Kare Hakkin Bil-Adama A Amurka

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version