Connect with us

TATTAUNAWA

Karya Ingila Ke Yi, Kirista Na Zaune Lafiya A Nijeriya –Dr. Abdul’azeez

Published

on

Wannan wata tattaunawa ce da MUHAMMAD ABUBAKAR ya yi da shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, Dr. BATURE ABDUL’AZEEZ, inda ya yi fashin baki kan irin halin da Kasashen Turai ke son jefa Nijeriya, ta hanyar yada farfagandar cewa ana kashe Kirista a Nijeriya.

Kwanan nan kasashen Turai na ta yawo da zancen cewa ana takurawa tare da kashe kiristoci a Nijeriya, me za ka ce?
Wato take-taken da Ingila ke kokarin yi na cinna wutar fitina. Sun dage suna yayata cewa Nijeriya ana kashe Kirista. Karya ne. Gwamnatin Nijeriya ko dabba ba ta kashe wa. Kashe-kashe ne na yanayi yadda ya kama a duniya ake ta faman yin sa. Idan ka dauki na Nijeriya, toh 75% na wadanda barnar ‘yan bindiga ta fi rutsawa da su Musulmi ne. Don haka ko 25% na kirista wannan lamari na kashe-kashe bai shafarsu. Babu hannun gwamnati a ko da 1% ne.
Akwai bukatar wayar da kan mutanenmu kan wannan makirce-makirce na turawa, musamman Ingila. Irin maganganun da ke fitowa daga Ingila karya ne. Su rika cewa wai a Nijeriya ana matsawa kirista, su dai a can ana matsawa bakar fata. A kullum ana kai hari a masallatai da sauransu kuma gwamnatin Ingila ba ta taba yin wani abu a kai ba.
Bayan an bada mulkin kai, daga baya kuma suka koma suna kulle-kullen munafurci, wato suka fara maganganu irin wannan cewar ana matsawa wata kabila ko mabiya wani addini. A Nijeriya ana zaman lafiya tsakanin ,musulmi da kirista. Hatta fadan da ‘yan siyasa ke hadawa a Nijeriya an riga an gane an waye shi ma an daina.

Kenan wannan kulli da a ke yadawa dadadden lamari ne?
Ingila a wancan lokaci, kowa ya san irin abin da ya faru tun daga 1965. Alamu da maganganu irin wannan da Ingila take yi. Irinsu aka rika yi, da irin haka da Ingila da Faransa su suka hada tuggu kan cewar a raba Nijeriya biyu, a yi yakin basasa, a yi yakin Biyafara. Bangaren Faransa suka dauki shugaba Sango na Senegal, su kuma Ingila suka dauki Julius na Tanzaniya. Wadannan mutane su suka zama karnukan farautar wadannan kasashe guda biyu, a takaice suna kai goro suna kai mari sai da suka kai ga sun hafda tuggun da wanda yake kukan ya ce an matsa masa. Abin da sai ya haifar da kisan mutane dubu darurruka a wannan yaki. Wanda ba kowa ya jawo ba, Ingila ne.
Toh yanzu wasu daga cikin ‘yan Nijeriya wadanda suna nan a cikin manyan ‘yan siyasan Nijeriya suna ta kulle-kullen tuggu suna sa wadannan yaran na Biyafara a gaba kan cewar su yi ta kukan cewa ana matsa musu, ana takura musu. Toh ai inda ake matsawa mutane Amurka ne da Ingila. Nan ne za a danne mutum yana wayyo Allah ba za a daga shi ba har sai ya mutu. Mu a Afirka ba mu da irin wannan, musamman a Nijeriya. Saboda haka muna fadakar da ‘yan Nijeriya irin wutar da Ingila take son cinnawa Nijeriya. Ko tausayi ba su jin halin da duniya ta shiga na Korona din nan, musamman su da suka ga zahiri suka ga ayar munafuki, ayar mai mugun nufi, bala’in da yake nemarwa mutane ya koma kansa. Ingilan nan a halin da ake ciki, mutane dama da 40, 000 suka mutum da korona, amma sun ki fuskantar matsalar da ke damunsu suna son sai sun kunno mana wata wutar rikici.
Su idan a baya sun yi mana mulkin mallaka, yanzu kuma mulkin me za su yi mana? Ai ba su da iko a kanmu, kawai ma muna basu girma ne a takaice. Amma zalunci da suka yi mana suka debe dukiyar kasa kafin su bada mulkin kai, ai ko sauraronsu bai kamata a ce mun yi ba. Amma sha’anin duniya ba haka yake ba.

Wanne kira ka ke da shi ga ‘yan Nijeriya?
Mu dai muna sanar da mutane akan a yi hattara, idan ba a manta ba tarihi ba ya goge kansa. A takaice kowa ya san Iraki, kowa ya san Saddam Hussaini. Ba wani ne ya cinna masa wuta ba, shugabannin Ingila ne suka cinna masa wuta suka yi karya suka fada wa duniya cewa yana da makaman nukiliya. Karya ne fa, suka sa aka yi masa taron dangi. Sai bayan an yi kaca-kaca da Iraki sannan aka gane babu wani nukiliya.
Kuma da gangan suka ce wai an kashe wasu mutane 40 ta hanyar iska mai guba, wadanda Turkawa ne. Wai kuma Amurka da Ingila ne za su bi musu hakkinsu. Toh ai kuwa mutanen da aka kashe a Iraki zuwa yanzu sun fi 400,000. Kuma a Iraki din nan tun 1990 zuwa yanzu har yau tana cikin yamutsi da hargitsi. Kuma su wadannan turawan suna jan fitinannu ne a jiki don bukatarsu ta biya.
Na tabbata ba a manta da irin abin da suka yi wa Gaddafi na Libya ba. Aka ce an kama mutane sai an yi musu shari’a, aka ce sai gaddafi ya biya diyya, ya biya. Amma a sharri irin nasu sai da suka yagalgala Libiya. Nan ma haka suke son yi mana kenan. Karshe a zo ana nadamar da ba ta da amfani.
Saboda haka ‘yan uwa ‘yan Nijeriya mu fadaka, Kiristanmu da Musulminmu mu gane turawan ba su sonmu da zamn lafiya. Kuma wadannan rigime-rigimen suna samun goyon bayan miyagun ‘yan siyasa ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: