“Da an fara daga safe har yamma, mutane suna zuwa suna kallon kaya suna tambaya, suna karbar adireshi, to ka ga duk kuwa Alhamdulillah, kwalliya ta biya kudin sabulu a kan wannan ziyarar.” Yadda Mista Saidu Mustapha, jami’i a kwamitin sa kaimin harkokin fitar da kayayyaki zuwa ketare ta Nijeriya(NEPC), ya bayyana a ziyararsa birnin Shanghai don halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin(CIIE) ke nan. Ya ce, yana sa ran kara halartar bikin a shekara mai zuwa.
A ranar 10 ga wata, an kawo karshen bikin CIIE karo na shida a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin.
- Afirka CDC Ta Bude Dakin Gwaje-gwajen Bincike Da Sin Ta Samar
- Bikin Baje Kolin CIIE: Kasashen Afirka Kar Ku Yarda A Bar Ku A Baya
A gun bikin na bana, ‘yan kasuwa daga Nijeriya sun baje kolin ridi da busashen citta da dawa da gyada da dai sauran amfanin gona da ma ma’adinai da ake samu a kasar. Ibrahim A. Ahmed, kwamishinan kula da harkokin cinikayya da zuba jari a karamin ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Shanghai ya ce, akwai kayayyaki da dama da suke shiga sahun gaba a Afirka ta fannin yawansu da ingancinsu, kuma CIIE ya samar wa Nijeriya wani dandali na nuna su ga duniya. Ya ce, “Shekaru shida a jere ne kasar Sin ta shirya wannan kasaitaccen biki na CIIE, wanda ya shaida niyyarta ta kara bude kofarta da ma habaka shigowa da kayayyaki, kuma hakan ya samar da damammaki ga kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa na habaka cinikinsu da ma janyo jarin waje.”
Ban da kayayyaki na Nijeriya, dimbin kayayyakin Afirka da aka baje kolinsu a gun bikin na wannan shekara su ma sun yi matukar jawo hankalin masu halartar bikin.
Idi Moussa Mahamadou, dan kasuwa ne daga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, wanda ya halarci bikin CIIE a karo na farko. Yawancin kayayyakin da ya kawo a wannan karo, amfanin gona ne, dake kunshe da dawa, da gyada, da zobo, da waken soya, da ridi, da zogale da kwaron arabic da sauransu. Ya ce yana fatan tallata kayan Nijar ga kasar Sin da ma duk duniya, don bada taimakonsa ga ci gaban kasar.
A cikin ’yan shekarun baya, kasar Sin ta yi ta sa kaimin shigowa da kayayyaki masu inganci na kasa da kasa, don duniya ta more babbar kasuwarta da ma ci gabanta. Tun daga shekarar 2018 kuma, kasar ta fara shirya bikin CIIE a farkon watan Nuwamban kowace shekara, wanda ya kasance irinsa na farko a duniya da ke mai da hankali musamman a kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare.
A bana, akwai kasashe 11 da suka halarci bikin a karo na farko, kuma daga cikinsu guda 7 kasashen Afirka ne. Karin kasashen Afirka da kamfanoninsu suna zuwa don nuna kayayyakinsu ga kasashen duniya. A cewar Stephen Kargbo, wakilin kungiyar raya masana’antu ta Majalisar Dinkin Duniya(UNIDO) a kasar Sin, dimbin kamfanoni na kasarsa, wato Saliyo, da na sauran kasashe daban daban dake nahiyar Afirka, sun halarci bikin CIIE na bana, inda suka samu damar nuna fasahohi, da kayayyakinsu a wannan muhimmin dandali na kasa da kasa. Ya ce, “Bikin CIIE na kasar Sin ya ba mabambantan kasashe damar more ci gaban tattalin arzikinta, kana kasar ba za ta bar kowa a baya ba.” (Lubabatu Lei)