Tambaya: Rahotanni na cewa, taron kolin rukunin G7 da ake gudanar da shi a Hiroshima na kasar Japan, ya fitar da hadaddiyar sanarwa da sauran takardu, inda aka zayyana batutuwan da suka shafi kasar Sin, tare da yin magana kan halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan. Shin Mene ne ra’ayin kasar Sin?
Amsa: Rukunin G7 na ikirarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, amma suna daukar matakan kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyya-shiyya, da hana bunkasuwar sauran kasashe. G7 ta yi biris da muradun kasar Sin, tana yunkurin sarrafa batutuwan dake shafar kasar Sin, da shafa mata bakin fenti, da tsoma baki a harkokin cikin gidan Sin. Saboda haka kasar Sin tana matukar nuna rashin jin dadi da kin yarda da hakan. (Amina Xu)