Yau Litinin 24 ga wata, hukumar sararin samaniyar kasar Sin, ta bayyana cewa, Sin ta baiwa Rasha da Faransa wasu samfuran sinadaran da aka debo daga duniyar wata a matsayin kyauta, yayin bikin kaddamar da harkokin murnar ranar sararin samaniya ta kasar Sin ta shekarar 2023.
A watan Afrilun da muke ciki ne, kasar Sin ta mikawa kasar Faransa samfuran sinadaran duniyar wata mai nau’in giram 1.5 domin ayyukan kimiyya, yayin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Sin.
Haka kuma, Sin din ta mikawa kasar Rasha samfuran sinadaran duniyar wata mai nauyin giram 1.5, domin aikin kimiyya a ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 2022, yayin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke gudanar da ziyarar aiki a Sin.
Bugu da kari, ita ma Rasha ta mayarwa kasar Sin samfuran sinadaran duniyar wata giram 1.5, don aikin kimiyya a matsayin kyauta, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar a watan Maris din bana.
A watan Disamba na shekarar 2020, hukumar sararin samaniyar kasar Sin, ta fitar da takardar dabarun kula da samfuran sinadaran duniyar wata, inda aka karfafa gwiwar nazarin samfuran sinadaran, a kokarin sa kaimi ga aikin more sakamakon kimiyya.
Ya zuwa yanzu dai, masu binciken kimiyya daga kasashen Australia, Rasha, Faransa, Amurka, Birtaniya da kuma Sweden, sun riga sun sanya hannu kan takardun aikin nazarin samfuran sinadaran duniyar wata na kasar Sin. (Kande Gao)