Kasar Sin ta fitar da ka’idojin dake mayar da hankali kan dabarun kula da muhalli na yankuna daban-daban.
Ofisoshin kwamitin tsakiya na JKS da Majalisar Gudanarwar kasar Sin ne suka fitar da ka’idojin cikin hadin gwiwa.
- Sin Ta Shirya Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2
- Rukunin Farko Na Masu Yawon Bude Ido Da Suka Samu Bizar Tashar Shige Da Fice Ya Isa Xinjiang
A cewar daftarin ka’idojin, abu ne mai muhimmanci a dauki dabarun kula da muhalli dake mayar da hankali kan yankuna daban-daban da kuma shata layi game da batutuwan da suka shafi kula da halittu da muhallansu da tabbatar da ingancin muhalli da kuma amfani da albarkatu daidai gwargwado.
Haka kuma, ya kamata zuwa 2025, a tabbatar da kaddamar da ka’idojin, sannan kuma zuwa 2035, ka’idojin za su taka rawa kamar yadda ya kamata daga dukkan fannoni.
Ka’idojin sun hada da dabaru 18 da suka shafi wasu bangarori 6, ciki har da inganta ci gaba mai inganci da tabbatar da kare halittu da muhallansu bisa ingantattun matakai da kuma karfafa sa ido da nazarce-nazarce. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)