Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a yau Juma’a ta fitar da wani rahoto da ya tona asirin asusun ba da tallafin dimokradiyya na kasar Amurka wato NED, inda ta kira ta dan aike na gwamnatin Amurka.
Rahoton mai taken “Asusun ba da tallafin dimokradiyya na NED: Abun da ya kunsa da kuma abun da ya yi” ya yi nuni da cewa, asusun NED ya dade yana kassara madafun iko a wasu kasashe, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe, da haddasa rarrabuwar kawuna da adawa, da yaudarar ra’ayin jama’a, da yin kutse na akida, duk a karkashin manufar inganta dimokradiyya.
- Kasar Sin Ta Yi Karar EU A WTO Kan Matakan Wucin Gadi Kan Motocin Lantarki Na Kasar Sin
- Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Masu Bayyana Ra’ayi Sun Zargi USADA Da Yin Rufa-rufa
La’akari da cewa, asusun NED a cikin ‘yan shekarun nan, ya ci gaba da canza salo, da kuma ci gaba da yin adawa da tarihi na zaman lafiya, da ci gaba da hadin gwiwar samun nasara tare, kuma ya yi kaurin suna wajen kutsawa, da kulla makarkashiya da yunkurin yin zagon kasa ga wasu kasashe. Rahoton ya jaddada cewa, munanan ayyukan asusun na NED sun haifar da babbar illa da janyo zargi daga kasashen duniya.
“Ya zama wajibi a tona asirin asusun na NED tare da fadakar da dukkan kasashen duniya, da kiyayewa da kuma yaki da tashe-tashen hankula da yunkurinta na zagon kasa, da kare ikon mulkin kasashensu, da tsaro da muradun ci gaba, da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya da adalci na kasa da kasa.” a cewar rahoton. (Yahaya)