Kasar Sin Za Ta Taimakawa Kasashen Musulmi Kara Karfinsu Na Yaki Da COVID-19

Daga CRI Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yiwa taron manema labaran da aka shiryawa karin haske game da yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin da bankin raya musulunci suka sanyawa hannu.

A cewarsa, bisa wannan yarjejeniya da sassan biyu suka kulla, kasar Sin za ta taimaka wajen samar da kayayyakin dakunan binciken yaki da annoba, da horas da jami’ai a kasashen musulmi 11 dake Afirka, domin taimakawa kasashen da abin ya shafa, kara karfinsu na yaki da annobar COVID-19.

(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version