Nahiyar Afirka ke a kan gaba a fadin duniya a mallakar ma’adanin gwal, kasashe da dama a Afrika na da ma’adanin gwal shifide a karkashin kasashen su inda masana suka kiyasta cewa akwai fiye da metreic tan 1000 na ma’adanin gwal a kasashen, wanda kuma hakan wata hanya ce na samun arzikin da zai iya jagorantar bunkasa tattalin arzikin nahiyar gaba daya.
Ma’adanin Gwal na da muhimmanci a fannin bunkasa kudaden Najiyar na kasashen waje, yana taimakawa wajen rage dogaro da karbar bashi daga kasashen waje yana kuma jawo masu zuba jari daga kasashen waje, haka kuma yana taimakawa wajen daidaita darajar takardun kudaden kasa.
- Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur A 2024 —Kyari
- Gidauniyar Ahmadu Bello Ta Gano Matsalolin Da Suka Addabi Ilimi A Arewa
Bayanai da suka fito daga wata kungiya mai zaman kanta da ake kira ‘Statista’ a binciken da ta gabatar a shekarar 2023, ta bayyana cewa, kasashen Afrika 10 da ke a kan gaba wajen mallakar ma’adanin Gwal sun hada da.
Algeria
Kasar Algeria ke a kan gaba a mallakin ma’adanin Gwal a fadin Afirka, inda aka tattabar da tana da Gwal da ya kai fiye da Metrik tan 174. Kasar ta fara cin cikakkiyar gajiyar ma’adanin Gwal din ne tun a shekarar 2000, an kuma kiyasta Gwal din da ke a karkashin kasa a kasar ya kai na Dala Biliyan 10.
Afrika ta Kudu
Kasar Afirka ta Kudu, ita ma na daga cikin kasashen Afirka da ke kan gaba a mallakar ma’adanin Gwal. Kasar na da fiye da Metrik Tan 125 wanda aka kiyasta ya kai na fiye da na Dala Biliyan 7.
Libiya
Kasar Libiya na da ma’adanin Gwal na fiye da Metrik Tan 117 wanda aka kuma kiyasta ya fi na Dala Biliyan 6.
An samu nasarar cin gajiyar ma’adanin Gwal a Libiya ne a zaman mulkin Marigayi Shugaba Gaddafi, amma tun bayan mutuwarsa da kuma yakin basasa da ta barke a shekarar 2011 ba a ci gaba da cin gajiyar ma’adanin Gwal din ba.
Misra
Kasar Misra na da ma’adanin Gwal fiye da Metric Tan 80.73 wanda aka kuma kiyasta ya kai na Dala Biliyan 4. Kasar ta samu karuwar ma’adanin a ‘yan shekarun nan, musamma a kan yadda take son ta canza akalar tattalin arzikinta da kuma kokarinta na rage dogaro ga kudaden ajiyarta na kasashen waje.
Marocco
Kasar Marocco na da fiye da Metrik Tan 22.12 na ma’adanin Gwal wanda aka kiyasta ya kai na Dala Biliyan 1. Kasar ta fara cin gajiyar ma’adanan Gwal dinta ne tun a shekarar 1970.
Nijeriya
Nijeriya na da fiye da Metrik Tan 21.37 na ma’adanin Gwal a karkashin kasa an kuma kiyasta ya kai na Dala Biliyan 1. An ci gaba da gano karin ma’adanin Gwal a sassan kasar a ‘yan shekarun nan, inda kasar ke neman ta kara hanyoyin samun kudaden shigarta don a rage dogaro da take yi a kan albarkatun man fetur.
Mauritius
Kasar Mauritius na da fiye da Metric Tan 12.44 na ma’adanin Gwal, kasar ta fara cin gajiyar ma’adanin Gwal din ne tun daga shekarar 1980, an kuma kiyasata Gwal din da kasar ta mallaka ya kai na Dala Miliyan 700.
Ghana
Ghana na da ma’adanin Gwal da aka kiyasta ya kai Metrik Tan an kuma kiyasata ya kai na Dala Miliyan 500. Kasar ta samu karin nasarar samun gano karin ma’adanin Gwal a ‘yan shekarun nan, tana hankoron kara bude hanyoyin samnun kudaden shiga ne don kawar da kai daga yadda take dogara da Koko, an kuma kiyasata ma’adanin Gwal din da ke shifide a kasar ya kai na Dala Miliyan 500.
Tunisia
Tunisia na da fiye da Metrik Tan 6.84 na ma’adanin gwal shinfide a cikin kasa an kuma kiyasata ya kai na Dala Miliyan 400, kasar tana cin gajiiyar ma’adanin ne tun daga shekarar 1970.
Mozambikue
Kasar Mozambikue na da mallakin ma’adanin Gwal na fiye da metrik Tan 3.94 wanda aka kiyasata ya kai na Dala Miliyan 200. Kasar ta kuma ci gaba da gano karin ma’adanin a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, inda take kokarin bunkasa tattalin arzikinta tare da rage dogaro da tallafi daga kasashen duniya.
Yadda kasashen Afirka ke kokarin ganin sun ci gajiyar ma’adanin Gwal a wannan lokacin wani alama ne na hankoronsu na fadada tattalin arzikin kasashen su da kuma kokarin su na rage dogaro ga tallafi da basuka daga kasashen Turai. Gwal na iya zama wata garkuwa ga kasashen Afirka na daukaka tare da gogayya da kasashe Turai a fage tattalin arziki duniya.
Karuwa ma’adanin gwal a Afirka zai taimaka wajen bukasa tattalin arzikin nahiyar gaba daya zai kuma kai ga bukasa kudaden kasashen waje tare da rage dogaro daga tallifi daga kasashe masu bayar da tallafi a duniya. Abin da ya rage a nan shi ne yadda gwamnatocin kasasshe Afirka za su tabbatar da cin gajiyar tare da amfanin da abubuwan da ake samu wajen bunkasa rayuwar al’umma Afirka ba tare nuna banbanci ba.