Bunkasar tattalin arziki shi ne gaggaurmin maganin yaki da talauci a tsakanin al’umma. A yayin da tattalin arzikin kasashen Afirka ke bunkasa sannu a hankali, suna taimakawa wajen samar da aikin yi ga dimbin matasanmu hakan kuma na daga darajar tattalin arzkin al’umma.
Bunkasar tattalin arziki kuma yana taimakawa gwamnati wajen samar wa da al’umma ababen more rayuwa kamar makarantu, kiwon lafiya, bayani ya kuma nuna cewa, samar da wadannan na taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma.
- AFCON 2023: An Fitar Da Jadawalin Zagaye Na 16
- An Maido Da Huldar Diplomasyiya Tsakanin Sin Da Nauru, CMG Ta Bude Ofishinta A Nauru
Wannan jadawalin kasashen da ake sa ran za su ci gaba a bunkasar tattalin arzikinsu a cikin wannan shekarar ya samu ne ta hanyar rahotannin tattalin arzikin Afirka daga Bankin Duniya na 2024.
Rahoton ya nuna kasashen da ake da kyakyawan zaton za su samu bunkasar tattalin arziki a shekarar 2024 in aka kwatanta da abin da suka fuskanta a shekarar 2023.
Rahoton ya nuna cewa, a kasashen Kenya, Egypt, Nijeriya, da Afirka ta Kudu sun samu zuba jari na kashi 68 a shekarar 2023.
Rahoton na yadda halin tattalin arzikin Duniya ke ciki ya nuna cewa, wasu kasashen Afirka za su samu gaggaurumin buinkasar tattalin arziki a shekarar 2024.
Kasashen da aka yi hasashen za su samu wannna bunkasa na tattalin arziki sun hada da 1. Mauritani da kashi 6.7, 2. Senegal da kashi 9.2. 3. Sudan ta Yamma da 2.5. 4. Comoros da kashi 3.6. 5. Uganda da kashi 6.1. haka kuma ana sa ran kasar 6.        Gambia za ta samu bunkasa da kashi 5.2. 7. Mozambikue da kashi 5.2. 8. Sao Tome and Principe da kashi 2.8. 9. Tanzania da kashi 5.9 sai kuma na 10. Malawi da kashi 2.0.
Tabbas wannan abin farin ciki ne in aka lura da yadda al’umma ke fargabar yiwuwar a tsumduma matsalar tattalin arziki a sassan Afirika, lallai wannan rahoto yana karfafa gwiwa.