Yusuf Shu’aibu da Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Kashedinku, Jan Kunnen Gwamnati Ga Masu Neman Sake Zanga-zanga

by Yusuf Shu’aibu da Khalid Idris Doya
February 12, 2021
in LABARAI
3 min read
Kashedinku, Jan Kunnen Gwamnati Ga Masu Neman Sake Zanga-zanga
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Tauna Aya…
  • Muna Da ‘Yancin Yi Daram – Masu Shirayawa

A yayin da wasu ‘yan Nijeriya da ke wasu sassan kasar ke kokarin sake gudanar da gagarumar zanga-zanga makamanciyar ENDSARS karo na biyu, gwamnatin tarayya ta yi kashedi tare da nanata cewa ba za ta lamunci wannan zanga-zangar a karo na biyu ba, a dai-dai wannan lokaci.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis. Ya bayyana cewa, baarin zanga-zangar ta gudana zai yi sanadiyyar rasa rayuwaka da dinbin dukiyoyi.
Mohammed ya ce, “babu wata gwamnati da za ta amince da halaka rayukan mutane da asarar dinbin dokiyoyi da yin kutse a cikin intanet kamar yadda ya faru a zanga-zangar EndSars a shekarar da ta gabata.
“Bayan haka, an halaka dan sanda guda daya da fararen hula guda hudu lokaci da aka kai hari ga ofishin Amurka a watan Janairu, wanda har yanzu ana ci gaba da farautar wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin samun damar gurfanar da su a gaban kuliya. Babu wata rai da take saman wata rai.
“Gwamnatin tarayya tana tunanin daukan gagarumin mataki a kan mabanbantan kafafan sadarwa na zumunta da ke kara rura wutar rikici a Nijeriya.
“Lallai kafafan sadarwa na zamani sun yi matukar tasiri wajen ruruta wutar zanga-zangar EndSars wanda ya faru a shekarar da ta gabata, sai da aka tashi tsaye kafin aka iya sawo kan lamarin.
“Ina fatan mun dauki darasi a kan zanga-zangar da ta gabata, domin haka ba za mu lamunci irin wannan lamari ba. Idan muka amince a lalata mana kasarmu, to mu ne za mu kwana ciki,” in ji ministan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, inda ya ayyana cewa babu wanda ya isa ya gudanar da wata zanga-zanga a Lekki Tollgate ranar Asabar, 13 ga watan Faburairun 2021. Ya nunar da cewa wasu tsiraru ne kawai ke neman fagewa da zanga-zangar ENDSARS don kokarin sake tayar da hargizi a jihar.

Kwamishinan wanda ya yi wannan furucin a yayin da ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Alhamis, ya lura kan cewa wasu ‘yan ta’addan sun kammala kimtsawa domin haifar da rashin kwanciyar hankali domin fakewa da wata zanga-zangar #EndSARS da aka taba gudanarwa a watan Okotaban da ta gabata.

samndaads

Kwamishinan ya ce sun kuma gano shirin wasu na kokarin tada wata zanga-zangar a jihar da zimmar neman kawo hargizi da yamutsi wa lamuran oda da oda, wanda kuma hukumar ta yi gargadin cewa kowa da wasa ba za ta lamunci hakan ba.

Ya ce, hukumarsu ta gudanar da bincike kan lamarin zanga-zangar inda wasu suka yi kokarin fagewa da zanga-zangar EndSARS domin cimma wata boyayyiyar manufarsu ta neman tayar da rigima a jihar Legas da kuma yada ta zuwa wasu sassan Nijeriya.

Daga bisani ya nemi hadin kan jama’a kan su mara musu baya tare da sanar musu rahoton dukkanin wani motsi da ba su amince da shi ba, sannan su kaurace wa shiga zanga-zangar da wasu ke kokarin shiryawa don tada hankulan jama’a.

Su kuwa a nasu bangaren, masu shirya zanga-zangar ta End SARS a karo na biyu sun bayyana cewa suna da ‘yancin yin zanga-zangar daram-dam-dam.
A cewarsu haramta amfanin asusun ajiya na cryptocurrency na dgaa cikin dalilan da suka sabba musu daukan matakin shirya sabuwar zanga-zangar.

Sun bayyana dalilansu ne a sanarwar manema labarai da suka fitar, da ke cewa dalilan shirya zanga-zangar ENDSARS karo na biyu.

Sun kuma nuna cewa akwai hukumomin tsaron da ke ta kokarin dakile shirinsu na yin zanga-zangar, kana rashin gamsuwa da hukuncin kwamitin bincike kan masu zanga-zangar ENDSARS da aka kashe a Lekki Toll Gate a ranar 20 ga watan Oktoban 2020 shi ma na daga cikin dalilinsu na himmatuwa wajen ganin sun sake shirya wani sabon zanga-zangar.

Sabuwar zanga-zangar da suka shirya a karkashin lemar #DefendLagos sun nuna cewa dole sai sun sake yin zanga-zangar, “Bayan kisan gillar masu zanga-zangar lumana da aka yi a Lekki Tollgate da wasu sassan jihar Legas, gwamnan Sanwo-Olu da wasu suna kokarin take lamurin kisan masu zanga-zangar da aka yi.

“Mu kuma mun ce ba mu yarda ba, ba za mu lamunta ba. Za mu sake mamaye Lekki Toll Gate a ranar Asabar 13 ga watan Fabrairu domin sake yin sabuwar zanga-zanga.”

SendShareTweetShare
Previous Post

Wata Sabuwa: Sheikh Abdujabbar Ya Garzaya Babbar Kotun Tarayya Ta Kano

Next Post

Gwamnati Ta Amince Da Shirin Kula Da Dattawa, Inji Minista Sadiya

RelatedPosts

Hadiza Usman

Hadiza Bala Usman Ta Yi Ta’aziya Ga Iyalan Marigayi Dikko Inde

by Yusuf Shu’aibu da Khalid Idris Doya
17 mins ago
0

Daga Abdullahi Sheme A ranar juma'ar da ta gabatane shugabar...

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

by Yusuf Shu’aibu da Khalid Idris Doya
25 mins ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Masana da masu ruwa da tsaki...

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

by Yusuf Shu’aibu da Khalid Idris Doya
2 hours ago
0

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa an ceto...

Next Post
Gwamnati Ta Amince Da Shirin Kula Da Dattawa, Inji Minista Sadiya

Gwamnati Ta Amince Da Shirin Kula Da Dattawa, Inji Minista Sadiya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version