Bello Hamza" />

‘Kashi 25 Na Mata Masu Juna Biyu Na Cikin Hadari A Nijeriya’

Daga Bello Hamza

Kungiyar fafutukar kayyade iyali “Association for the Adbancement of Family Planning (AAFP)” ta bayyana bukatar kara ilimantar da alumma a kan hanyoyin kayyade iyali musamman saboda bincike ya nuna cewa, rayuwar kashi 25 na mata masu ciki a Nijeriya ke cikin mummunan hatsari.

Shugaban kungiyar AAFP, Farfesa Oladipo Ladipo, ya bayyana haka a taron manema labarai da kungiyar tayi a Abuja, ya ce, masu cikin Na cikin mummunan hatsarin da zai iya kai wa ga rasa rayukan matan ko kuma ya haifar musu da matsalolin da zai iya shafan rasuwarsu gaba daya.

Ya ce, mata nasu ‘ya’ya da yawa kamar abin daya fi 4 ko kuma mata masu daukar ciki kafin su cika shekara 18 da haihuwa zasu iya fuskantar cucuttuka da dama,  suna kuma iya rasa ransu gaba daya.

Ya ce, rashin bayar da tazarar haihuwa da kuma mata masu  daukan ciki bayan sun wuce shekara 35 da haihuwa, yana barazana ga rayuwar mata don yana haifar mummunan sakamako.

Ladipo Ya kuma shawarci mata dasu rinka saurin fara haihuwa, misali daga shekara 20 zuwa 29.

Ya lura da cewa, ya kamata duk matan da take kokarin yayin da ta kai shekara 35 a duniya ta tabbatar data yi ragista da asibitin dake da kwararrun ma’aikata domin lura da ita yadda ya kamata saboda kaucewa duk wani matsalar dake zai iya tasowa.

Ladipo ya kuma bukaci kafafen watsa labarai dasu ilimantar da jama’a da kuma canza tunaninsu a kan bukatar takaita iyali da mahimmanci iyali dan kadan domin a cimma rayuwa cikin koshin lafiya da karuwar arziki.

“Hanya daya da za a cimma wannan manufan shi ne canza tunanin jama’a, za kuma a fi samun nasarar wannan lamarin ne ta hanyar amfani da kafafen watsa labarai.

“Idan kafafen watsa labarai suka fito da hatsarin dake tattare da yawan jama’a musamman ga tattalin arzikin kasa, jama’a zasu yi gaggawar rungumar tsarin kayyade iyali dai dai da yadda gwamnatin tarayya ta amince.

“Yawan yaran da aka amince iyali su haifa shi ne yara hudu tsakanin mata da miji amma dokan na nufin yara hudu ga namiji ba wai yara hudu ga kowacce mace ba.

“Idan mutum nada mata biyu, zai zama kowacce mata zata haifi yara biyu kenan, Idan kuma kana da mata udu ne ya zama kowacce mace zata haifi da daya kenan,  ta haka zasu samu rayuwa mai inganci ba tare da takurawa ba” Inji shi

Exit mobile version