Hukumar Kididdiga ta kasa (National Bureau of Statistics), ta shelanta fitar da kashu na kimanin naira biliyan 146.1 zuwa kasashen waje a cikin watanni shida kacal.
Rahotan ya bayyana cewa, kashun na kimanin naira biliyan 102.3; an fitar da shi ne zuwa Kasashen Kudancin Gabashin Asiya.
Adadin kashun da aka fitar a wata shida na shekarar 2023, ya haura wanda aka fitar a shekarar 2022 zuwa kasashen wajen na kimanin naira biliyan 116.
- Sojoji Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Kama Barayin Mota 3 A Bauchi
- Za A Binciki Yadda Aka Karkatar Da Tallafin Korona Naira Biliyan 183.9
Idan za a iya tunawa, Shugaban Cibiyar Habbaka Fita da Kaya Kasashen Waje (NEPC), Dakta Ezra Yakusak, a watan Afrilu ya bayyana cewa, Nijeriya ta fitar da kashu na kimanin naira biliyan 116, wanda ya yi daidai da Dalar Amurka miliyan 252 a shekarar 2022.
Shugaban ya kara da cewa, kididdiga ta bayyana fitar da wannan kashu a matsayin na biyar cikin albakatun kasa da ya fi kawo wa Nijeriya kudin shiga baya ga man fetir a shekarar 2022.
Har ila yau, Sakatare Janar na kungiyar masu harkokin kashun ta Nijeriya, Sotonye Anga ya bayyana cewa, kashi 90 cikin 100 na masu noman wannan kashu tare da fitar da shi zuwa kasashen waje, na fitar da shi ne tsuransa; wanda hakan ya sa ake ta faman tafka asara a duk yayin da aka zo fitar da shi zuwa kasashen na waje.
“A duk yayin da muka fitar da tsuran kashu zuwa kasashen waje, kamar muna yin watsi da ayyukan yi ne ga matasanmu ko kuma muna samar wa wasu kasashe da ban ayyukan yi a lokaci guda.
Don haka, muke kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, su yi kokari wajen habbaka tare da gyara wannan masana’anta, domin ci gaban kasa da samar da ayyukan yi da kuma sauran masu aiwatar da wannan sana’a baki-daya,” a cewar tasa.
Haka zalika, Sakatare Janar din ya kara bayyana cewa, har yanzu Nijeriya ba ta iya sarrafa sama da kashi 10 cikin 100 na wannan kashu, shi yasa suke kira ga gwamnatin da ta himmatu wajen kokarin gyara tare da fara sarrafa ko da kashi 30 ko 50 ne cikin 100.
Sannan, idan har za a bai wa wannan masana’anta ta kashu kulawar da ta dace, ko shakka babu Nijeriya za ta iya samun kudin shiga da ya kai kimanin biliyan 30 zuwa 200 nan da shekaru biyar masu zuwa, wanda hakan zai ba wa masana’antar damar shiga cikin jerin sahun gaba na wadanda suka fi bai wa Nijeriya gudunmawa na kudin shiga, a cewar ta Anga.