Kassu Zurmi fitaccen ma kadi ne, amma a bangaren kidin maza. Tubalan da a ke amfani da su wajen kidan maza su ne zuga da kirari da kambamawa da kwarzantawa da kasada da sai da rai.
Jaridar leadership Hausa ta tattauna da Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji kuma kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Zamfara, don jin waye Kassu Zurmi tasowarsa da shahararsa da wake-wakensa har zuwa rasuwarsa. Alhaji Ibrahim fitacce ne mai bayar da gudunmawa a kan wakokin ba ka, musamman wadanda su ka shafi Zamfara da Sokoto da kewaye. Duk da kasancewarsa fitaccen dan siyasa wanda ya rike mukamai da dama, amma wannan bai hana shi ba da dukkan gudunmawa da bibiyar wakokin ba ka na gargajiya ba tare da yi mu su hidima.
Ranka ya dade, wa ne Kassu Zurmi?
Kakansa Gandau ya taso daga Kurawa ya je wani gari da a ke kira Dumfawa ta masarautar Morikia karamar hukumar Zurmi a jahar Zamfara. Gandau mahaucine har ya kai ga sarautar Sarkin Fawa ya na kidan fawa da bori ya na kada duma. Bayan rasuwar Gandau sai Amadu ya tashi daga garin Dumfawa ya koma Magarya a masarautar Zurmi a nan ya haifi Abuba kar Kassu Zurmi. Kassu da ya tasa ya kai shekara 15 sai a ka fara ganin abubuwa da ya nuna na yana son ya gaji mahaifinsa a kidan fawa da bori yana kada duman girke.
Mahaifin Kassu ya tashi daga Magarya ya koma Kadawa amma zaman bai yi masa ba sai ya dawo Magarya amma a lokacin shi Kassu sai ya yi zamansa a Kadawa gun kanin mahaifansa mai suna Abdullahi ya ci gaba da hidima tai ta noma da kuma kidinshi. Ya na tara abokanansa yana yi musu kida da baki yana so su yi fada don ya ga jarimi a cikinsu. A ha ka ya ci gaba da kidan noma da bori da wannan abin kidan wato duman girke.
Ta ya ya ya samu sunan Kassu?
An kira shi da Kassu ne saboda an haife shi ne ranar kasuwar magarya don ha ka a ke kiransa da Mai Kasuwa sannu sannu sai a ka gajarce mai Kasuwa a ka koma ce masa Kassu. Ana kuwa hada sunansa da Zurmi saboda inda duk ya zauna daga Magarya da a ka haife shi da Kadawa inda ya zauna har Allah ya yi masa rasuwa duk suna karkashin masarautar Zurmi ne.
Yaushe ya fara kidi da waka?
Karen mata mai farin kunkuru
Na ga gidanku akwai manya
Kowadda ka tana ‘yamma ka tulle
Daga nan likkafa ta ci gaba, Kassu ya fara wakar tauri da kafar dama hatta kai ya sha gaban duk wani mawaki da ya yi suna a wakar tauri.
Akwai abokin Kassu a kauyen Gandasamu wanda a ke kiran sa da Dodo. Shi Dodo gidansu kidin kalangu a ke yi sai Kassu ya nemi su hadu su yi guruf ha kan kuwa a ka yi sai suka hada kungiya da ’yan gidan su Kassu ’ya’yansa da kannensa cikin ’ya’yansa akwai marigayi Umaru Kaho da Usman Da Rabi’u da Abdullahi da na gidan su Dodo. Sai su ke kira karkashin shugabancin Kassun su na yi ma sa kida ya na yi mu su waka.
Kassu ya yi fice a wakar tauri. Wakar Tauri waka ce ta tsiya wadda a ke yi wa matsiyata. In an ce Tsiya a tauri a na nufin fita daji da jarumtaka da tashin hankali da jajircewa wanda a ke samunta ta hanyar asirai da na saiwowi da na uhammadiyya da asirrai don ka hau da suna ,ba ana nufin tsiya ta rashin arziki ba. Fitacciyar wakarsa akwai wakar Shayi Dan Gidan Labbo. Kassu Zurmi ya yi wakoki da daman gaske. Akwai wakanda a ka saka ma a faya-faye da kuma wadanda ba a dauke su ba. Amma dai ta faifai ya na da sama da dari biyu. A cikinsu akwai:
- Wakar Ibrahim Shaho
- Maidabo na gidan Duwa
- Waakar Garu-garu na Mande
- Wakar Basara ke
- Wakar Labbo na Gandau Jabanda
- Wakar Auta baban suri
- Wakar Rabi’u dan manyan matcata Rawayya
- Wakar Musa na kasar dan Ali
Da sauransu.
Kassu ya rasu yana da kusan shekara Saba’in a shekarar 1983. Har yanzu akwai zuriyarsa a Kadawa, amma gidansa na Kadawar yanzu ya koma karantar Islamiyya.
Shin Kassu ya sami magaji a zuriyarsa a harkar waka?
Eh, bayan rasuwar Kassu dansa Umaru Kaho shi ya ci gaba da jagorantar wannan gidan sai dai bai yi nisan zango ba ya rasu. Bayan rasuwarsa sai dan’uwansa Malam Usman to amma shi Malam Usman bai bi hanyar waka ba shi ma malami ne har sai da ya zama Limamin masallacin garin Kadawa kafin ya rasu. Yanzu akwai yaransa guda biyu da suke jagorantar Hizba a wannan yanki na Kadawa. Akwai Rabi’u wanda ya ke yin wa’azi a masallacin Kadawa kafin liman ya shigo.
Mai kuge uban ‘yam malam,
Gojen hwad’a Karen D’an Ali,
Twasshi Kai a Uban Dawakin Sababi radda ba ka ba wani goje.
An Kai Malami Garin ya Zanna,
Hak ka tashi rena garin mu?
Wanga gari ba aiki an dai izo ni bakin Daji.
Twasshi yacce Kai Malam ka an hank’ure a tadda hwarauta
bana ni d’ai ina cika ka da aiki,
Don mi?
Sai nai hwad’an zube ban kwarya.
Twasshi kuma mi ah hwad’an zube ban kwarya?
Kassu Kasan hwad’an zube ban kwarya?
Tadda wanga, tallabi wanga, ga wani can ana gadon d’auko shi,
Shi ah hwad’an zube ban kwarya.
Ran nan kan mutum D’ari ni ka ba ka in ba guda ka tambayo Mainasara.
Twasshi en man,
In da za a Kai ka a Kai ka,
Ka yo wadda tab buwayi shari’a,
Wadda za a taso ma gida ba a dariya ba a da ka,
Dada ba a san wadda za ayi ga gari ba.
A tasamma Kanwurin dan Ali yace kashedi – kashedi a wuce shi da sheri
A yi kaura ga Buba kar na Muhamman shi kau yace kashedi – kashedi
A wuce dasu asasu motat en’a a wuce a kaima Garba na Ukku,
In an kazo a bashi ta kadda ya tallabe ta ya duba kaji yace
La’ilahaillallahu Muhammada Rasulallahi halan ‘Yan Birnin Magaji sun kunyi halinku?
To, ni ma ba ni son ganin kahurci,
A wuce da su a kai ma Bature,
Mai Ja kadai ka enmasu Oda,
Su Samu Sallal layya arba’in basu gida,
Da sun sha Kunun hwada ya ishe su.
Kui ta abin ku yan kananan tauri,
Kui ta abin ku tun da ba a hwarauta,
Amma hwa ba ruwan masu gari,
Ko can gadauniyak kuce kananan tauri,
Wadan ga’yan kanana – kanana,
Kun ji wadanda nah hana mu hwarauta,
Babu ruwan masu gari,
Ka ga kato ko maganin Jini bai sha ba wai sai dadin kidi ya sa shi hwarauta,
Sara guda ya hwadi ya mike sai ka ji an ce an kashe wane ba a koma hwarauta,
To kunji wadanda nah hana mu Wala.
Yaro bai zo K’uris ba ko Gambiro ko Baras ko Rayya ko Zari Mai k’azamin Daji ko ko mutun ya zo Kan yaro,
Wai Kan ki gayya,
Kaji in da a ka taron sababi in an ka ce ana Kan yaro,
Ko hwarautar Kizni ko hwarautag Geza ko Mutun yazo
Hana Wanka ko Dogon Hwako ko hwarautar yar koliyal
Ko an yi yar jini cikin Dutcawa ko Dutsin dari cikin Hwadamawa
Koko a kwana babban tabki can gabas ga tabkin Hili a gangarikke Hwadama,
Ha! Ko a dawo nan gabas in an kazo baras ko rayya
A ce za a ‘yar madoka ko’ yar Kuna ko hwarautar mai kamar rini ko a tai hwarautar geza
Ko a tai hwarautar Zurmi a Kwan Dumburun a rab’o daji,
Ko ko nan azo Dirau ko Dassai ko a tai hwarautar Shamusalli Babban Daji asha ruwa gabas ga yi na ka,
Can in da ba ka Jin bari wane,
Ba ka jin saki wane,
Sai dai ka ji jidat wuka ga jikin ka.
Wannan sai su dakikki dakikki daki kasa da kasa gobara taho kiyi kunya,
Tai can bisa runhwa,
Kaza Mai diya ka tsoron shaho in don kudukku sai tayi shanya.
Kassu abin da yassha kaina kowa yana kirarin tauri,
Da wanda yaggada hadda wanda bai gada ba.
Banza taurin yaro da yayyi ba ya da asali,
Yaro ko yayi tauri bai da Uba Kututu,
Icce ko baya tciri ba saye,
Allah waddan abin da baya da tushe,
Maganin kwarai sai gado,
Gidan Goga ku da kun ka san shi ku gane,
Kun ji kalangu yace ga Kututu ga Kututu.
Na Dodo mai Uba Kututu,
Anne kahi kyau kana huntunka,
Buzu yace an hi son ka dokad daji,
Bare ace tana kware ta hwad’i in da kahirin mu ka iko.
Na Dela ba haushi ba a ce ma ka don mi?
Banawa Birnin Magaji ba ta da hanya,
Ban ni in kida masu dud wanda bai sani ba ya san su,
Tun zamani su Mani A kaye hat tak kai ga zamanin Mai Sabra,
Hat tak kai ga zamanin Mainasara hag ga Na Dodo Dan kanen Mainasara.
Rantsuwa sabatta iyali,
Dan Mutuwa wanda ba a yaye ga gida,
Ko an yayai ba ya mance mamma ya Koma
Bakon Magaji mai cika aiki,
Twasshi bakon karen bunu mai sa a kai ma likkita jinya,
Ko likkita sai ya Koka,
Sai ya Koro wadanda su kwashe da ciyo,
Kai ba magani,
Ku tai gida ya k’are (gaishe ku yara!)
Don Na Dodo nik Kwan Katcina han nikkwan Wagini garin D’an Ani
In da ba a k’aryag Giwa,
Yaro in ka yi gardama a ja ka a kai ka in ba giwad dawa ba giwag dawa.
Nik Kwan gidan su Ya’u Bature,
Ya’u jikan hwari,
Bakon gidan Ayi dan magajin Rogo,
Bakon gidan su Idi Achali,
Bakon gidan su Atti na Duna,
Na kau roki gahwara ga Aminu sai mun dawo.
Domin agogo mai cika aiki,
Taro dole zan yi yiwa Twasshi Kidi abin kidi ya ka bani.
Alwashin maza karen dan Ali,
Don na Daudu mai cika aiki,
Tonka ka biya ni ba ka da bashi.
Uban gidansu Dije da mota,
Uban gidan su Igge Sa kakka Komi nib bida yana iya bani,
Ka ji wadda hayyata tacce,
Tace ana Koma yi man wani doki,
Twasshi mu zo garai anai mani doki.
Ina na Dela ba haushi ba a ce ma ka don mi,
Karen na Daudu ban ci Sabo,
Ban ci dai akwai sani da amana da Birnin Tsaba ba su Koma hwarauta,
Na hwad’a masu wa ac cikin su mai iya Yak’I,
Kadan ne,
Ba ni son kadan na ta hwarmai,
Cikin guma -gumai ni ka kai shi a dai kai mai babba mai cika mashi hannu,
Ya na saran Maza ya na hutawa.
So mu kai nasara ta tashi,
Kai masu yaya daji,
Ku zan ki busa,
Ku kau magabatan gari ku ban mu hwarauta,
Da an yi ba sani ba Sabo,
Duk wanda bai shira ba ya shirya.
Ba a wane bara na,
Ba a wane babba na ne,
Ba nawa bana bata sanyi bata Siyasa,
Ba a tsaya na san ka,
Babu gahwara ba sarbo,
Babu wane kau aboki na ne.
Bana duk wanda bai shira ba ya shirya,
Taho na Dela bahaushi ba a ce ma ka don mi,
Tonka ka bayani ba ka da bashi Tonka,
Ga Dugaji,
Ga Dugaji in ji mutanen Katcina.
Lallai Honourable, ka sha harda. Mun gode kwarai da samun lokaci da ka yi mu ka tattauna har da tsarabar wakar Kassu.
Ni ma na gode, Allah Ya sa wa wannan sabon tsarin na jaridar LEADERSHIP A Yau albarka.