Katsina 2018: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya?

Daga  Yazidu Nasudan

Da yawa dai Hausawa kan ce komai nisan dare gari zai waye. Taro dai an riga an yi shi, ya wuce koda yake dai ba za a rasa yan korafe-korafe ba nan da can, wasu daga ciki na gaskiya ne, wasu kuma irin wadanda a ka san dan adam da su ne wadanda ba su da tushe.

 

Nasarorin Da Taron Ya Samu

A ganina taron ya samu nasarori guda uku: Nasara ta farko ita ce duk bakinmu da su ka taho daga wurare daban-daban, sun iso lafiya cikin yardar Allah, an yi taro lafiya, kuma kowa ya koma gidansa lafiya, ba mu samu labarin wani ko wasu ya samu wata matsala a hanya ba. Lallai godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki bisa wannan ni’ima tasa, kuma cikin ikonsa da kaddarawarsa ne dukkan bakin namu su ka zo lafiya su ka kuma koma gidajensu lafiya.

Nasara ta biyu da taron ya samu ita ce haduwar dimbin masana masu tarin yawa daga bangarori daban-daban, musamman Farfesa Abdulkadir Dangambo, Farfesa Ibrahim Malumfashi, Farfesa Ibrahim Birniwa, Farfesa Salisu Yakasai, Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, Dakta Bishir Abu Sabe, Dakta Aliyu Idris Funtua, Dakta Jibrin Hussaini, Dakta Abdurrahman Ado da dai sauran manyan masana da su ka hallara. Lallai tara wadannan a wuri guda ba karamin al’amari ba ne.

A cikin jawabinsa, babban bako mai jawabi, wato Farfesa Ibrahim M Malumfashi, na jami’ar jihar Kaduna ya yi tariyar baya ne ta hanyar tsunduma wa da mahalarta taron cikin kogin tarihi, shehin malamin ya dauko batun tun daga tushe inda ya bayyana cewa Hausawa asalinsu daga wani yanki su ka fito na Asiya, kafin suka iso inda su ke a yanzu bayan tafiya da dogon zamani mai cike da cin zango.

Haka kuma ya yi cikakken bayani dangane da yadda adabi ya doru da tsira a cikin alumma, shehin malamin ya yi nuni da cewa babu wani abu wai shi kirkirarren labari, sai dai dole marubuci ko marubuciya su kan rubuta ko dai abinda su ka ji, ko su ka gani ko kuma abinda su ka gada a cikin jininsu.

Kasancewarka kusan dukkan masanan sun tofa albarkacin bakunansu, inda aka tattauna sosai a kan muhimmancin da irin gudummuwar da marubuta za su iya bayarwa domin ciyar da al’umma gaba.

Nasara ta uku da taron ya samu, ita ce ta amsa kiran da dimbin marubuta da ‘yan jarida daga ko’ina suka yi, su ka halarci wannan taro mazan su da matan su, manyan da kanana, babban abunda ya fi burge ni shi ne, samun damar halartar da iyayenmu su Dan’azumi Baba Cediyar ’Yan Gurasa, Ummaru Danjuma Katsina ( Kasagi ), Injiniya Musa Abdullahi, da Ado Ahmad Gidan Dabino (Mon) Da Sule Maje Rejeto da Hajiya Halima Sarmai Daga Nyame da Alhaji Kabiru Assada, Malam Kabiru Ana, Malam Mansir Daga FCEKAT da dai sauran manyan marubuta daga ciki da wajen kasar nan.

 

Babban abinda mahalarta taron su ka fi korafi a kai shi ne, rashin ba wa marubuta fifiko a wurin taron, maimakon haka sai aka fi maida hankali a wurin bayar da dama ga makada da mawaka suka barje guminsu, wanda hakan ne ya sa wasu daga cikin marubutan da abin bai yi wa dadi ba, suka rika tambayar, wai taron makada da mawaka ake yi ko taron ranar marubuta a ke yi?

Amma daga bisani jagororin taron sun kare kawunansu ta hanyar kafa hujjar cewa da mawaka da marubuta uwarsu daya ubansu daya, kuma ba zai yuwu a iya raba su ba.

Haka nan kuma wani kalubale da mahalarta taron su ka lura da shi shi ne na rashin halartar sarakuna na Katsina da Daura ko kuma wakilansu. Haka kuma ba a ga manyan jami’an gwamnatin jihar a wurin taron ba, sai dai kawai lokacin taron bada kyaututtuka.

Haka nan ba a ga dandazon mahalarta taron daga cikin jama’ar gari ba. Kamar ma mutanen gari ba su san a na yi ba, wanda hakan na nuna cewa sashen hulda da jama’a na taron bai yi aikinsa yadda ya kamata ba.

Wani babban kalubale da taron ya hadu da shi kuma shi ne, na rashin samun dakin taro da wuri, domin da farko har an buga katunan gayyata da sunan dakin taro na sakatariyar gwamnatin jiha, amma daga karshe wurin bai samu ba, kusan sai ana saura kwana daya taron sannan aka samu tabbaci dangane da dakin taron da za a yi amfani da shi.

Tun farko da babban kwamitin shirya taron ya yi aiki da shawarwarin da karamin kwamiti mai kula da walwala da tsare-tsare ya bayar na yin amfani da dakin taro na kudi, maimakon dogara a kan na gwamnati da ba a samu wannan matsalar ba.

Haka kuma wani karin kalubale da taron ya hadu da shi shi ne, na karancin kudi, musamman saboda tallafin gwamnatin jiha bai samu ba har zuwa lokacin fara gudanar da taron kuma kusan wannan tallafin shi ne babban abinda masu shirya taron su ka zura idanu su na jira, sai ga shi kuma bai samu ba.

Tururuwar da marubuta su ka yi domin halartar taron shi ma wani kalubale ne, domin an samu akalla kusan marubuta 250 da su ka iso birnin Katsinawa tun a ranar Juma’a, saboda haka sauke mutane masu irin wannan yawan da ba su abinci da sauran abubuwan da rayuwa ke bukata har na tsawon kwanaki biyu ba abu ne mai sauki ba.

Sannan kuma wani abun dubawa shine irin yadda taron ya yi shakulatin bangaro da jarumar da ta yi sanadiyyar assasa taron tun farko, wato Fadila H. Aliyu Kurfi. Abin mamaki ne a ce ko a cikin takardar tsarin jaddawalin taron sam babu sunanta kuma ko sau daya taron bai ambaci sunanta ba. Tabbas wannan babban butulci ne da babu wani abinda ke haddasa shi idan ba hassada ba. Koda yake dai Hausawa su kan ce, ba a sauya wa tuwo suna. Saboda haka ko an ambaci sunan Fadila H. Aliyu Kurfi ko ba a ambace ta ba, ko an ba ta wata kulawa ko ba a ba ta ba, babu wani mahaluki da ya isa ya sauya tarihin cewa ita din dai ce ta yi sanadiyyar assasa wannan abun alherin da wasu su ke ta dagawa su na hura hanci da shi.

Haka nan wani abinda ya so zama cikas ga taron shi ne hatsaniyar da ta biyo bayan wata magana da mai gabatarwa ya yi a wurin taron bada kyaututtuka da ya gudana ranar Asabar da daddare, wato Malam Nasir Wada Khalil, inda ya danganta marubuta da makaryata. Hakan ya yi matukar bata ran wasu da dama daga cikin mahalarta taron.

A karshe kamar yadda babban bako mai jawabi, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya fada; lallai taro ya yi albarka. Don haka mu na kira da a taro na gaba a yi kyakkyawan shiri kuma a kan lokaci, domin kauce wa irin matsaloli da kuma kalubalen da a ka fuskanta a taron bana.

 

Jinjina Ga ’Yan Babban Kwamiti

Shugaba Rabiu Naauwa

Nasir Wada Khalil

Bilkisu Yusuf Ali

Fadila H. Aliyu Kurfi

Sa’adatu Saminu Kankia

Auwal Ibrahim Danborno

Sakataren Sufi

 

Jinjina ta musamman ga wadannan mutane, wadanda tabbas ba don su ba, wallahi taron nan da bai yiwu ba:

Malam Danjuma Katsina

Dakta Bashir Abu Sabe

Malam Abdurrahman Aliyu

Kwamared Lukman Umar Kankia

Aisha Muhammad Sabitu Mobil

Bishir Sulaiman (Bash Twins )

Fatima S. Muhammad

Fadila H. Aliyu Kurfi

Yazidu Nasudan

 

Godiya ta musamman da jinjina ga Hajiya (Dafta) Bilkisu Yusuf Ali. Lallai iliminki ya yi ma ki amfani. Na jinjina ma ki.

 

Haka kuma mu na kara mika matukar godiyarmu ga:

Alhaji Kabiru Dankaura, Fagacin Katsina, Hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano

Alhaji Isa Saidu Barda

Alhaji Lawal Katsina

Hukumar Samar da Ruwa ta Jihar Katsina (RUASSA)

Hon. Ibrahim Kalil Aminu (SA Youth Debelopment)

Dakta Aliyu Idris (Probost FCE Katsina)

Alhaji Aminu Danbaba

Dikko Kofar Sauri

Justice Musa Danladi Abubakar

Alhaji Shamsu

Makera Motel

Maikudi Hotel

Godiya ta musaman ga dukkan bakin da suka samu damar halartar wannan taro, da fatan Allah ya maida kowa gidansa lafiya.

Exit mobile version