Sheikh Muhammad Mahi Inyass khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya aike da rubutacciyar wasiƙar taya murna cikin harshen Larabci ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
A cikin wasiƙar an rubuta saƙon taya murna zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano, kuma Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass (Allah ya kare ka).
Ga cikakkiyar fassarar wasiƙar:
- An Shawarci Sarki Aminu Ado Ya Fice Daga Kano
- Wata Sabuwa: Kotu Ta Hana Aminu Ado Da Sauran Sarakuna 4 Kiran Kansu Sarakuna A Kano
Amincin Allah da Albarkarsa da kuma jinkansa ya tabbata a gare ka.
Bayan haka,
A wannan al’amari na sake dawowarka zuwa ga kujerar magabatanka masu martaba, ina mai farin ciki da samun zarafi, a madadina, da dukkan iyalan Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) domin bayyana farin ciki da murna da fatan alkairi gare ka Mai Martaba.
Kamar yadda muke taya ka murna cikin wannan al’amari na farin ciki, kuma muna sake jaddada goyon bayan mu gare ka, tare da umartar masoyanka da Muridai da su sake maka mubayi’a domin ci gaba da jagorantarsu bisa tafarkin iyaye da kakanninka, wanda zai shiryar zuwa ga tafarkin cin nasara da ya ginu akan karfafa gwiwa da himma domin samun nasarar cimma burin hadin kai a dukkanin sassan Nigeria.
Bisa ga wannan al’amari, ya kai Mai Martaba Sarki, kuma Khalifan Shehu Ibrahim A Nigeria, ina mai tunatar da kai, Allah ya taimakeka, wani zance daga wata wasiƙa ta shugabana, Shehina, kuma Mahaifina ya rubuta zuwa ga masoyinsa kuma abin soyuwarsa Marigayi Kakanka Alhaji Muhammadu Sanusi Bayero, faɗinsa cewa: Dukkanin jama’ar Africa na buƙatar tabbataccen hadin kai kamar Nigeria, ku haɗu da kowa cikin gaskiya da haɗin kai da hakuri.
Haka nan muna tare da dai zuciya da ruhi cikin wannan babbar manufa, kuma muna fata (Manufar) zai cika dukkanin fatan Musulmi tare da kai, ta hanyar ɗaga tutar Musulunci da ka gada daga magabatanka masu daraja.
Allah mai iko ne akan yin komai.
Da aminci.
Daga Sheikh Muhammad Mahi Ibrahim Inyass, Khalifan Sahibul Faydha, kuma hadimin al’umma.
Alhamdulillah.