Daga Rabi’u Ali Indabawa,
Babban Khalifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, ya yi addu’a ta musamman ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki.
Khalifa Sheikh Mahi Inyas ya yi wannan addu’a ne a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai wa Dakta Saraki a gidansa da yake unguwar Maitama a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja.
A yayin ziyarar, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ne ya fara jawabi da neman a yi addu’ar neman rahamar Allah ga Marigayi tsohon Khalifan Tijjaniya ta Duniya wato Sheikh Ahmad Tijjani bin Ali.
Bayan sun yi addu’a ga ruhin Marigayi tsohon Shugaban na Tijjaniya, sai sabon Khalifa Sheikh Mahi ya bayyanawa Dakta Saraki irin ayyukan da yake gudanarwa a kasar Senegal. Musamman ma batun harkar noma da yake yi.
Khalifa Sheikh Mahi ya ce; “Na shiga harkar noma ne domin samar da ayyukan yi ga matasanmu na yankin Afirka ta Kudu. Wannan zai sa su samu abin yi a yankin namu, ba sai sun rika yunkurin shiga kasashen turai ko ta wanne hali ba.
“A yunkurinsu na son shiga kasashen Turai ta kowanne hali ne sai ka ga suna ta rasa ransu, wasu kuma ka gansu a wulakance,” inji shi
Shi ma a nashi jawabin, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya yi godiya tare da nuna matukar farin cikinsa da wannan ziyara ta Khalifan na Tijjaniya. Sannan ya nuna farin cikinsa ga irin addu’o’in sa albarka da Khalifan ya yi masa.
Daga karshe dai Khalifa Sheikh Mahi ya tattauna batun yadda za a kyautata alaka tsakanin Tafiyar Tijjaniya ta duniya da Nijeriya.