A karon farko tun bayan barin ofis a shekarar 2021, tsohuwar shugabar trashoshin jiragen ruwa na Nijeriya NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman ta yi bayanin yadda tsayuwarta na ganin ana gudanar da harkokin hukumar yadda ya kamata ya yi sanadiyyar jire ta daga mukaminta, musamman yadda ta ki amincewa da biyan fiye da Dala miliyan 22 don kwangilar yashe kogin Kalaba da kuma kwangilolin da suka shafi INTELS suka yi sanadiyyar ta rasa aikinta a mastayin shugabar Hukumar ta NPA. Hajiya Hadiza ta yi wadanna bayanan ne a cikin sabon littafin da ta rubuta mai suna “Stepping On Toes: My Odyssey At The Nigerian Ports Authority”.
Tsohohuwar shugabar tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), Hadiza Bala-Usman ta bayyana cewa, sake sabunta wata kudin kwagilar yashe kogi da ta gyaran Jiragen Ruwa ne hummulhaba’sin ya sa tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya sauke ta daga kan mukaminta.
- An Bude Bikin Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Fitarwa Daga Kasar Sin Karo Na 133
- Masallacin Ƙudus Na Musulmin Duniya Ne – Mabiya Shi’a
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, an dakatar da Bala-Usman a watan Mayun 2021 biyo bayan zargin gazawar tura kimanin Naira biliyan 165 zuwa ga asusun a kudin shiga na tarayya na CRFA.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da dakatar, inda aka bayar da umarnin a binciki asusun na hukumar NPA da Amaechi ya yi a lokacin yana ofis.
Ministan ya kuma kafa kwamitin don a gudanar da bincike akan harkokin hukumar, cikin har da kwangilolin da aka bayar daga 2016 zuwa watan Mayun 2021.
Sai dai, Hadiza Bala-Usman a cikin wani sabon littafinta da ta rubuta mai taken” Taka Sahun Wasu: Dogon Zangon da na yi ina shugabancin NPA”, ta nuna jayya da tsohon ministan kan wasu manyan ayyukan hukumar.
A cewarta, sabon littafin ya yi banai dalla-dalla akan abubuwan da suka faru da kuma rikice-rikecen da suka kunno kai a kokacin ina shuabantar hukumar ta NPA.
Ta ce, masu ruwa da tsaki a fabbin sufiri sun gargade ta cewa, ministan na son ganin an kore ta a lokacin da ake shirin sake sabunta wasu manyan kwangiloli biyu masu mahummanci. Hadiza Bala-Usman ta ci gaba da cewa,“Na farko shine, kucem yashe kogin na biyu kuma kwangilar aikin gyaran Jirafen ruwan”.
Ta kuma gabatar sa bukar wa’adin kudi ga kanfamonin wa’adin don yin yasar ba tare da bin ka’ida ba.
Ya samu amincewar dawo da kwagilar gyaran Jiragin Ruwan.
Ya samu hakan ne ta hanyar kamfanin da ke bin gwamnatin tarayya bashi, bisa saba tsarin tura kudi zuwa cikin asusn bai daya na TSA da kuma yiwa hukumar ta NPA kwangila.
Hadiza Bala-Usman ta kuma yi ikirarin cewa, ta yi wata tattaunawar sasanci da ministan, inda Amaechi ya soke ta da rubutawa shugaban kasa wasika kai tsaye ba tare da sanar da ministan ba a matsayin sa na ministan da ke sa Ido a ma’aikatar ta sufuri ba.
A cewarta, ministan ya shiga gabanta a saboda haka bai son yaga ta ci gaba da zama rike mukaminta, inda kuma ta sheda mata ta ajiye mukaminta ko kuma yakalubalanci dakatar da ita a gaban Kotu.
“Na sheda masa cewa, bubu daya da zan yi daga cikin wadannan abinda ya bukaci in yi, musamman ganin cewa, an kafa kwatitin da zai gudanar da bincke.”
“Gwamatin tarayya ba ta karbar ajie aikin ma’aikacin da ke fuskantar bincike. Na yi amannar cewa idan na yi daya daga cikin wannan, zai kaance tamkar na amsa lafina ne. Na sheda masa cewa ba zan yi ko daya daga ciki ba, amma zan kwamtin binciken ya kamala aikinsa tare da abatar da bincikensa, an bani tabbacin cewa, babu wani laifi da na aikata.”
Bayan da taki amincewa da shawarar ta Amaechi, Hadiza Bala-Usman ta yi ikirarin cewa, tsohon ministan daga bisani ya sheda mata cewa,“ Zai tabbatar an ci gaba da gudanar da binciken har zuwa 2022, a yayin da aka fara gudanar da hada-hadar siyasa don kar shugban kasa ya tuna cewa, har yanzu ina akan dakatarwa. Ya ce, abinda ya fi mayar da hankali akai shine, ni a yanzu ga shiugabar NPA bace.”
Hadiza Bala-Usman ta karkare cewa,“Duk da shiga tsakani a cikin magara da kungiyar gwamnonin APC Amaechi ya dage Kai da Fata, sai an cire daga kan mukamin shugabancin NPA”.
Kalamanta, “Wasu kungiyoyi da ke da ra’ayi da shugabannin APC suma sun yi kkarin shiga tsakani. Na san misali gwamonin da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar APC, da gwamna Atiku Bagudu ke shugabanta, sun tattauna akan maganar dakatar dani sun kuma kafa kwamitin da zai shiga tsakani.”
“Tawagar gwamnonin sun gana da ministan don lalubo da mafita kan maganar. Amma ya hakikance dole ne sai an binciki shugabancin da na yi a NPA saboda gazawar tura harajin da ake turawa gwamnatin tarayya kudi CFR. Har kokarin zuga gwamnoin ya yi inda ya sheda masu cewa kasafin kudin hukumar ta NPA ya fi kasafin kudin akasarin jihohin a saboda haka, karsu wani tausaya min.
“Bayan da gwamnonin suka dage, ya sheda masu cewa, maganar ba ta kuma a gabansa sai dais u je gun shugaban ma’aikata na tarayya.
Hadiza a cikin sabon litattafin nata ta ce, “ Ministan ya kuma shedawa wani mutum da ya yi kokarin shiga tsanaki kan maganar cewa, ni na cka son kaina, bana tura masa wani alheri daga NPA kuma ban taba bashi kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa ba. “