Soja mai matsayin Kofur, John Gabriel, mai lambar aiki ; N/A13/69/1522, ya bayyana dabarun da ya yi amfani da su wajen yaudarar fitaccen malamin nan dan Jihar Yobe, Sheik Goni Aisami-Gashua, kafin ya yi masa kisan gilla.
Daily Trust ta rawaito cewa, tunda farko dai sojan ya bukaci Malamin da ya taimaka ya rage masa hanya gabanin ya kashe shi a daren ranar Juma’a.
- An Shiga Alhinin Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Sheikh Goni Aisami Gashuwa, A Yobe
- Tilas Ne Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Mataki Kan Kisa Sheikh Aisami – Sheikh Bala Lau
Lokaci Sheikh Aisami ya baro garin Nguru yana tunkarar Gashua lokacin da sojan ya bukaci ya karasa da shi zuwa Jaji-Maji.
A lokacin da suke kan hanyarsu ya bukaci malamin da dakata ya duba motarsa ya ji tana kara, motar da bai sake komawa ba kenan ya bindige shi.
Sojan ya bayyana hakan ya yin da yake amsa tambayoyi a hannun Jami’an ‘Yansanda a ranar Laraba, aojan wanda yake aiki a karkaahin runduna ta 241a garin Nguru, ya ce Sheik Aisami ya yi masa wasu tambayoyi biyu kafin ya ja kunamar bindiga ya harbe shi har lahira.
“Lokacin da na daga bindiga ta na saita shi sai ya tambaye ni cewa me na yi maka? ” sai na ba shi amsa cewa babu abinda ka yi mun. Sai ya sake tambaya ta cewa, ‘Kana son ka kashe ni ne?’ sai nace masa, ‘A’a ba kashe ka nake son yi ba.’ Sai ya yi shiru, sai na dan yi harbin Jan kunne haka, zatona zai firgita ya gudu. Sai ya ki guduwa. A Lokacin da yake kokarin komawa motarsa kawai saina saita shi na bindige shi.”
Kisan gillar malamin ya tayarwa da mutane da dama hankali a fadin Nijeriya tare da bukatar lallai a hukunta masu hannu a ciki.
A wata tattauna da shugaban kungiyar Izala na kasa, Bala Lau, ya yi da sheahin Hausa na BBC ya yi Allah-wadai da kisan ya kuma bukaci abi kadin jinin malamin, Inda ya bayyana kisan a matsayin ta’addanci.