Ga akasarin ‘yan Nijeriya rahoton da aka wallafa na kashe jami’ian ‘yan sanda 229 a cikin watanni 22, wani abin damuwa ne.
Wadannan alkalumman sun nuna yadda, aka samu raguwar jam’ian da ke rike da manyan mukamai da suka kai kaso goma a cikin wata.
- Tallafin Wutar Lantarki Ya Kai Naira Biliyan 199.64 A Nijeriya – NERC
- Yadda Ciniki Ya Habaka Tsakanin Babban Yankin Kasar Sin Da Yankin Macao A Fiye Da Shekaru 25
Wannan ta’addacin da aka yi wa wadannan ‘yan sandan da suka rasa rayukansu, babban abin damuwa ne, kuma abu ne, da ba za a lumunta ba, kuma dole ne, a gudanar da bincke, duk da cewa, duk wanda aka dauke shi aikin wanzar da tsaro, zai iya rasa ransa, ako wane lokaci.
Amma wannan zafin rashin na jami’an, duk da cewa, mutuwa wata aba ce, da ba za a iya kaucewa mata ba.
Wasu rahotannin sun bayyana cewa, adadin na wadannan mamatan ‘yan sandan, ko dai ‘yan bindiga daji, ‘yan bindiga, ‘yan kungiyar ta’addan Boko Haram, ‘yan kungiyar asiri da kuma masu fashi da makami ne, suka yi salar salwantar da rayukansu.
Sun dai, rasa rayukansu ne, a yayin da suke kan gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Duba da wannan rahoton za a iya yin tunanin irin yawan ‘yan Nijeriya da ba su ji, ba su kuma gani ba, suka rasa nasu rayukan, duk a cikin wadannan watannin 22.
‘Yan Nijeriyar sun rasa rayukansu ne, ba wai domin sun aikata wani laifi ba, sai dai kawai, domin wasu ‘yan siyasa masu rike da madafun iko ne, ke shugabanta su, ba su dauki rayukansu a bakin komai ba.
A Nijeriya abin ba a boye yake ba, domin aikin na ‘yan sandan kasar tamkar sadaukar da rai ne, musamman ma da yadda suke yin artabu da miyagun masu aikata manyan laifuka a yayin gudanar da aikinsu.
Wani abin bakin ciki shi ne, a yayin artabun, miyagun sun kasance suna dauke da manyan makamai ne, da suka fi na ‘yan sandan, wanda a wani lokacin, hakan ke bai wa miyagun galaba, a kan ‘yan sandan a lokacin artabun.
Wannan jaridar ta dade tana maimaita maganar cewa, akwai matukar bukatar a wadata jami’an ‘yan sandan kasar nan, da manyan makamai, idan ka yi la’akari da irin hadarin da ke tattare da aikinsu.
Wani abin takaici shi ne, yadda mahukuntan ‘yan sanda a kasar, ba su bai wa ‘yan sanda wadatattun Albarusai, wanda kuma ake kakaba masu takunkumin dole ne, sai sun sanar da hukumomin ‘yan sandan, adadin Albarusan da suka yi amfan da su a yayin da suke gudanar da aikinsu, na kwantar da duk wata kura, da ta taso.
A rubuce yake a kasar nan cewa, a daukacin bangaren jami’an tsaron kasa, bagaren ‘yan sanda, sune koma baya wajen rashin kula da jin dadinsu da walwalarsu.
Wannan matsalar, ta kasance tana karya masu gwiwa wajen gudanar da aikinsu a cikin nuna kwarewa, domin yiwa alumma aiki yadda ya dace.
A wasu lokutan ma, sune suke sayawa kansu kaki da wasu manyan kayan aiki, domin kawai, su gudanar da aikisnu, na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Sai dai kuma, wannan ya tabbatar da maganar mu, duba da yadda ake wadata su da manyan makamai idan an tura zuwa wasu kasashe don tabbatar da zaman lafiya.
Kazalika, wani abin dubi shi ne, yadda ‘yan sandan suke gudanar da aikinsu, ba tare da suna da wata kwarewar kirki ba, koda yake, wasu na cewa, haka irin aikin nasu yake, amma mu ana nan, muna da jayya kan wannan ra’ayin, domin kuwa, ba irin aikin ‘yan sanda bane, a cikin tawargar su, su rinka farautar manyan masu aikita laifi, a cikin motocin su da suka riga suka tsufa ba.
Babban hatsari ne ga ‘yan sanda su fita gudana da aiki da Albarusan da aka kidaya masu, za su yi amfani da su ba.
Hakazalika, bama goyon bayan cewar da ake yi ‘yan sandan su kula da jin dadinsu da walwalarsu da kansu, domin kawai, Babban Sifeta Janar na ‘yan sanda ya amince masu su sanya kaki.
Dole, a a tabbatar da ana kula da sa kishin kasa, musamman a aiki irin na ‘yan sanda, duba da irin barazanar da suke fuskanta a yayin gudanar da aikinsu.
Suma ‘yan Adam ne, kamar kowanne dan kasa kuma suna da iyali da ‘yan uwa, da suka dogara a kansu.
Mun dade muna ankarar da hukumomin tsaro na kasar nan, kan kalubalen da hukumomin tsaron kasar ke ci gaba da fuskanta, wanda irin wadannan kalubalen, an kirkire su ne kawai.
Kazalika, akan kuma samu takardama ko rashin jituwa, a tsakanin wadannan hukumomin tsaron kasar, wanda kamata ya yi a ce, sun hada kansu a waje daya wajen samun bayanai.
Yin amfani da fasahar kimiyyar zamani wajen samun bayanai na sirri, a tsakanin hukumomin tsaron kasar, na daya daga cikin abubuwa masu mahimmanci.
Domin gudanar da aikin, ba tare dayin dabarun samun bayanan sirri ba, tamkar fargar daji ne.
A ra’ayin mu, babu wani dalili da zai sanya a ce, an rasa rayukan ‘yan sandan kasa, a cikin wannan gajeren lokacin.
Muna ganin ya zama wajibi, mahukutan ‘yan sandan kasa, su tabbatar da sun dauki matakan da suka dace, wajen kare rayukan jami’an.
Kazalika, muna son mu kara nanata cewa, aikin ‘yan sandan ba wai aiki ne, na jeka ka kashe kanka ba, kuma bai katama a rinka yiwa aikin kallon haka ba.
Ba da ce, ace aikin ne, na mutuwa domin kare kasa ba, kamata ya yi, aikin ya zamo aiki ne, na kare kasa kuma jami’I ya kasance a raye, domin ya sanar da labarin.