Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji-Kontagora, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan al’amuran da suka faru na mutuwar ASP Shu’aibu Sani Mulunfashi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda DSP Nafi’u Abubakar kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
- Barazanar Harin Abuja: ‘Yan Ta’adda Ba Sa Bayyana Lokaci Da Wurin Kai Hari – Shehu Sani
- Da Dumi-Dumi: Bankin CBN Zai Sake Sauya Fasalin Naira N200, N500 Da N1,000
Wanda a ranar 19 ga Oktoba, 2022 da misalin karfe 2:10 na rana , wani ASP Abdullahi Garba, jami’in ‘yan sanda na Sauwa, ya samu sabani da ASP Shu’aibu Sani Malunfashi, jami’in sashen binciken aikata laifuka na II, hedikwatar ‘yan sanda ta Argungu, a wajen kamun kifi na garin Argungu. A dalilin haka ne suka yi artabu da juna a gaban shagon ASP Abdullahi Garba.
A yayin da ake fafatawa, ASP Abdullahi Garba ya yi amfani da almakashi ya daba wa ASP Shu’aibu Sani Malunfashi a hakarkarinsa na hagu. Da samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na Argungu, sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka damke jami’in da ya aikata laifin.
Bisa ga hakan ne aka garzaya da ASP Shu’aibu Sani Malunfashi zuwa Asibitin tunawa da Sarki Yahaya da ke Birnin Kebbi, inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Sakamakon haka, jami’in ‘yan sanda da ya aikata laifin, ASP Abdullahi Garba, aka tsare shi a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Birnin Kebbi, yayin da kuma aka mika binciken nasa zuwa sashin kisan kai domin gudanar da bincike mai zurfi don gano musababbin lamarin.
Kazalika, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kebbi ya aike da tawagar manyan jami’an ‘yan sanda domin ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokan arziki wanda ya rasu tare da addu’ar Allah ya jikan Asp Shu’aibu Sani Malunfashi ya gafarta masa.
Bugu da Kari CP Ahmed Magaji Kontagora ya kuma yi Allah-wadai da matakin da jami’in da ya yi kuskure ya nuna wanda ya saba wa koyarwar ‘yan sanda da dokar ‘yan sanda da kuma sauran dokokin da suka shafi kundin kasar Nijeriya.
Hakazalika, CP ya gargadi jami’an rundunar da su zauna lafiya a kodayaushe tare da kai rahoton korafe-korafen su ga sassan da suka dace a cikin rundunar domin gyara a maimakon daukar doka ga hannu.
Daga karshe kwamishinan ya tabbatar wa da jama’a cewa, za a yi adalci wajen gudanar da bincike kan lamarin sannan kuma za a bayyana sakamakon binciken.