Ci gaba daga makon jiya
Abinci
Kwararru sun bayyana cewa abinci da kayan marmari suna da matukar muhimmanci ga lafiyar kowane Dan’adam. Sun kara bayanin cewa abincin da ake ci na zamani da ke kunshe cikin kwali ko gwangwani wadanda suka kunshi sikari, mai kitse, suna taimaka wa wajen yin teba ko kiba wadda ba ta da misali da kuma kawo cutar zuciya.
Don haka sai suka yi kira da a kara shan kayan marmari masu yawa da cin ganyayyaki da wasu kayan abinci da suke dauke da dussa ‘fibre’ da sinadaran ‘minerals’ da za su taimaka wa lafiya.
Masana kiwon lafiya sun yi kira da mutane da su rika shan ruwa a kalla lita uku a kowace rana, inda suka ce hakan yana taimaka wa ruwan jiki da sauran wasu abubuwa.
Har ila yau, sun kuma bayar da shawarar rage cin abincin da ke kara kuzari ‘carbohydrate’, haka nan mai kitse sai dai a rika hadawa ganyayyaki masu yawa domin hakan na taimaka wa wajen rage kuzarin da yin wani abu kan sikarin da ke jikin mutum.
Haka nan, Dakta Omotola ta ce da yake ana kara samun ilimin da ya shafi abinci, “Mun gano cewa irin abincin da muke ci yana da amfani musamman idan ana maganar lafiyar jikinmu. Akwai wasu nau’o’in abincin da suke da ‘casino genic’, ma’ana suna taimaka wa wajen kamuwa da cutar kansa.
“Sai dai kuma kash! nau’o’in abincin su ne wadanda yawancinmu muka fi bukata amma suna cutar da mu. Kamar cin jan nama da kayan lemu masu sikari da zaki, su ne wasu daga cikin abubuwan da ake ke jin dadin ci da sha. Haka kuwa akwai al’amarin abincin da ya kunshi sinadarin kitse ‘fat’ da hukumar lafiya ta duniya da sauran masu fada a ji suka ja kunnen mutane dangane da cin su.
“Abin farinciki da wannan labari ya nuna da akwai wasu nai’o’in abinci da suke maganin kamuwa dacutar kansa. Kamar kayan marmari da ganyayyaki suna matukar kyau ga lafiyarmu. Idan mutum yana cinsu kowace rana, yana kare kanshi daga kamuwa da kansa, saboda su kayan marmarin sun kunshi sinadarain ‘fibre’ da yawa, musamman ga wadanda suka kai shekara 50 ko fiye da haka.
“Haka ma tumatari ma ya kunshi wasu sinadarai da suke maganin kansa da amfani da tafarnuwa da albasa ba kawai suna kara wa abinci armashi ba ne, su ma suna da sinadaran yaki da kansa. Karas yana da amfani wajen yaki da cutar kansa, haka nan ma lemon zaki da na tsami. Mun yi sa’a a Nijeriya saboda wadannan abubuwan ba wuyar samun su ake yi ba.
“Ko da yake wadanda suka riga suka kamu da cututtuka kamar hawan jini da ciwon siga, abu mafi dacewa ne a ce abincinsu ya canza da yadda suke tafiyar da rayuwarsu. Idan kuma wanda bai kamu da daya daga cikin cututtukan ba, matukar har ana son kare kani daga kamuwa, ya kamata a sha lita uku ta ruwa kowace rana. Ya rage cin kwai da rage cin abincin da yake da mai da abinci mai sa kuzari, ya ci abinci da ya kunshi sinadarin ‘bitamin’, sannan ya rage cin gishiri.
Wadannan su ne abubuwan da za su taimaka wajen hana kamuwa da daya daga cikin cututtukan.”
Motsa Jiki
Motsa jiki akai- akai wani babban mataki ne kasancewa cikin koshin lafiya da kuma hana kamuwa da matsalolin da suka shafi lafiya, kamar yadda Dakta Obiora ya bayyana.
Ya kara da cewa wani al’amari na daban kuma, mutane da yawa ba su motsa jiki kullun wanda wannan shi ya sa suke kasance a yanayi na iya kamuwa da cutar sikarai ta 2.
“Mu yi iya bakin kokarimu na tabbatar da kuzarin da muke samu ta hanyar abinci mun kona shi, idan ba mu yi haka ba, muka ci gaba da tara kuzarin zai kasance sinadarin ya kai ga yi mana yawa, daga nan kuma sai ta rika taruwa a jikinmu.
“Motsa jiki yana da amfani ya dace mu rika yin hakan a kalla minti 30 kowace rana na gudun sarsarfa, ta a kalla sau biyar a kowane mako, wannan zai ba da minti 150 na motsa jiki a kowane mako. Hakan zai taimaka idan mun samu damar motsa jikin da ya zarce hakan yana da kyau.
“Matakan su ne, ya dace mu rage yadda muke tafiyar da rayuwarmu, mu yi kokari na yin tattaki na a kalla 10,000 kowane mako. Idan muka yi hakan zai nuna mun yi abin da ya dace domin za mu iya. Sai mu yi kokari wajen yin tattaki fiye da 10,000 kowane mako, wannan abin da ake so ne domin zai sa mu kasance cikin lafiyar zuciya”
Tsafta
Haka kuma kula da tsafta kamar wanke hannu akai- akai da rufe baki lokacin da ake yin tari da hamma, yin wadannan abubuwa suna da muhimmanci wajen hana kamuwa da cuta da sauran matsalolin da suka shafi lafiya. A cikin wadannan za mu yi cikakken bayani kan kowanensu da samar da hanyoyi na canza dabi’un rayuwarmu da suka shafi kula da lafiya.
Tabbatar da tsaftace muhalli ciki da waje, sai kuma mutum ya kula da tsaftace kan shi, wannan yana da muhimmanci ya dace a yi kokari wajen ci gaba da kiyaye su cewar Obiora.
Damuwa
Yadda mutum yake yi lokacin da yake cikin wani hali na sai ya yi wani abu ko fuskantar matsalar ko kuma a yi masa wata barazana. Hakan na faruwa ne lokacin da muka samu kanmu cikin yanayin da ba mu za ta ba. wannan shi ne babbar matsalar da take shafar lafiya. Bincike ya nuna cewa shiga yanayi na damuwa kan iya samar da ciwon kai, rikicewar ciki da na jini, ciwon kirji da matsala lokacin barci.
Kamar yadda kwararre babban jami’i na kula da lafiyar yara da harkar lafiya, Dakta Yashua Alkali Hamza, ya bayyana cewa shakatawa tana da muhimmanci kamar yadda mutuwar farad daya take saboda tsayawar bugun zuciya sakamakon hawan jini, wadannan duk abubuwa ne na matsalar da ke shiga lokacin damuwar.
“Mutane su yi kokari su koyi yadda za su daina shiga halin damuwa, domin damuwa ita ce sanadiyyar kamuwa da rashin lafiya, abin bai tsaya sai a cutar zuciya ba har ma da sauran wasu cututtuka.
“Lokacin da ka shiga halin damuwa sai a hana kwayar halittarka mai yaki da abin da zai cutar da kai. Don haka idan mutum bai san yadda zai yi ya fita daga cikin halin da ya shiga ba, sai a karshe abin yana iya damun lafiyarsa.”
Ya ba da shawara kan yadda mutum zai yi ya fita daga cikin halin damuwar. A cewarsa, ka yi kokari yadda za ka iya ka hana kanka shiga halin damuwa duk da yake ana cikin wani mawuyacin hali, amma ya kamata ka samu lokacin dai za ka dan nimfasa ka sake dawo da hankalinka wuri daya, ka daure wajen yin duk yadda za ka yi ka rabu da damuwa.
Ya ce mutuwar farar daya da ake samu da tsayawar bugun zuciya da hawan jini duk suna da alaka da al’amarin da ya shafi rayuwa.
Shan Taba/Giya
Al’amarin shan giya, an gano cewa shi ne babbar matsalace da aka gano ita ce sanadiyar kamuwa da cutar ake iya maganinta da kuma hanyar kamuwa da cutar da a sanadiyar mutuwa a duniya. Hakanan ma akwai cututtukan da suke shafa hanta da sauran cututtukan da sike da alaka da abubuwan da suke taimakawa wajen shaka da fitar iska, sai kuma mutuwar barin jiki.
Yawan shan giya na iya samar da matsala ga hanta ko lalacewarta, shan kwaya da yiyuwar kamuwa da nau’oin cutar kansa, wannan ya hada da kansar mama da ta hanta.
Cibiyar kula da al’amuran da suka shafi giya ta bayyana cewa shan giya da bai wuce ka’ida ba shi ne kwalba daya ga mace, yayin da shi namiji zai iya shan kwalba biyu kowace rana.
“Ga wadanda suke shan taba, shan taba dabi’a ce da ke da matukar hadari. Su ma wadanda suke shan giya idan har abin ya zama dole ka da su wuce fiye da unit 21 hakan na nufin kwalba uku kowane mako, wannan ga namiji kenan, idan mace ce ka da ta zarce kwalba biyu a mako kamar yadda aka jaddada”.
Bacci
Bincike ya nuna cewa samun damar yin barci kamar yadda ya dace yana sawa a samu yanayi mai gamsarwa na ciki da wajen mutum ya zama lafiya ba wata matsala. Idan ba a samun isasshen barci ba, yana iya kai wa ga yanayi na kasala, babu maida hankali kan abin da mutum yake yi da karuwar yiyuwar samun hatsari har ma da matsalolin da suka shafi lafiya kamar kiba maras misali da kuma kamuwa da ciwon siga ta 2.
Obiora ya ce “Ya kamata mutum ya rika samun yin barci na awa 8 kowace rana ga babban mutum, idan ba a samun yin isasshen barci hakan na iya sa a kamu da cututtuka. Don haka tsaftar barcinmu ita ce mu yi barci kamar yadda ya dace, hakan zai taimaka wajen rage damuwarmu da yiyuwar kamuwa da cuta mai matsala.”
Wani likita mai suna Dakta Salau Adeeso ya ce ana samu karuwar matsalolin hawan jini a Nijeriya daga kashi 8.2 a shekarar 1990 zuwa kashi 32.5 a shekarar 2020. Haka nan ma daga miliyan 4.3 da suka kamu da cutar a shekarar 90 abin ya karu da mutane miliyan 27 a 2020. Kamar yadda ya ce fiye da kashi 29 ne suka san da cutar a jikinsu, yayin da kashi 12 suna kan shan magani.
Kwararre masanin kwayoyin cutar, Dakta Uche Uwajeh ya ce matasa masu shekara 20 yanzu suna kamuwa da hawan jini saboda wadannan dalilan, shan muggan kwayoyi, shan giya, rashin aikin yi, rashin albashi mai tsoka, matsalar tattalin arziki, rashin tsaro, son sai an yi arziki ko ta halin kaka musamman saboda matsin abokai.
Sabon binciken da ba dade da wallafawa ba a sabuwar mujallar zuciya ta Nahiyar Turai ta bayyana cewa da akwai alaka tsakanin amfani da waya da hawan jini. Binciken an yi shi ne bayana da aka samo mutane 212, 046 wadanda suna daga cikin ma’aikatan ‘Biobank’ na Ingila.
An bayyana cewa hawan jini ya shafi miliyoyin mutane kuma an ta’allaka shi da matsalolin da suka shafi lafiya, wadanda suka hada da tsayawar bugun zuciya, hawan jini, yiwuwar kamuwa da cutar mutuwar bangaren jiki, sai bata lokaci mai yawa wajen amfani da waya, an alakantasu da taimaka wa kamuwa da cutar hawan Jini.
Masu binciken sun gano bata lokaci mai yawa wajen amfani da waya kowane mako, yin haka na iya kusantar kamuwa da cutar hawan jini. Akwai masu bata fiye da awa shida a kowane mako da suka kai kashi 25 na yiwuwar kamuwa da hawan jini.