Ko Ka San Illolin Sauyin Yanayi?

Tare da Umar Saleh Ankausanka01@gmail.com      08036005151

Masana sun yi hasashen cewa, kasashe masu tasowa su ne za su fi fama da matsalolin da suka shafi canjin yanayi kama daga kaura, kwararowa hamada, ambaliya ruwa , karancin ruwan sama dama ruwan sha sakamakon kafewar koguna da rashin tsaro ga kuma uwa uba tsananin talauci masana yanayi sun yi hasashe cewa mutane kusan biliyan daya ne canjin yanayi zai tilastawa barin yankunansu ko ma kasarsu baki daya. Kasashen da ke cikin hadarin fadawa wannan matsala kuwa sune kasashen Afurka da wasu kasashe a gabaci da kudancin Asiya. Musamman illar tafi nunawa a kasashenmu na Afurka sakamakon rashin hanyoyi masu sauki na noma da kiwo wanda hakan na zama barazana ga ci gaban tattalin arziki da walwalar mazauna wannan yanki na bakaken fata, misalai da daman a nuni ga hakan sakamakon rashin kasar noma da yanayi mai kyau da makiyaya zasu sakata su wala dasu da dabbobinsu  za mu iya gane illar canjin yanayi daga fadace -fadace da ke faruwa a wasu sassa na Nijeriya tsakanain manoma da makiyaya wanda hakan ya zama ruwan dare a wurare kamar su Filato, Binuwai , Taraba da sauran yankuna da suke da danshi kuma da albarkatun dazuka da koramai wanda hakan shi ne babban dalilan da ya sa makiyaya ke kwarara zuwa wadannan yankuma domin samun abinda dabbobinsu za su ci duk da cewa ana alakanta rikicin da cewa siyasa ce ta kawo hakan, karancin ruwan sama na tilastawa makiyaya matsawa da mahaifarsu zuwa wajen da za su samu isasshen abinci da zasu ci da dabbobinsu.

Kasashe kamarsu Nijar da kamaru da Cadi na fama da illar canjin yanayi idan ka dubi arewacin Jamhuriya Nijar za ka samu kauyuka da dama da babu wani babban namiji a gida domin yawancinsu sun gudu zuwa birane domin samun abin rufin asiri , canjin yanayi na barazana ga tsaro da tarbiya yara harma dana manya domin sakamakon kaura da mazaje ke yi yawancin yaransu na rasa kulawa ta musamman daga iyaye sakamakon rashin zaman gida da iyayyensu basu samu damar yi ba , sanadiyyar wannan hali da muka tsincikai Nijeriya wadda ita ce babbar kasa a Afurka ta yi fama da tashe-tashen hankula sakamakon hare-hare na ‘yan tada kayar baya daga Boko Haram wanda hakan baya rasa alaka da aikin yi ga samari har ma da tsofaffi, hakan kuma yajawo koma baya ga tattalin arziki, lafiya da kuma dakile cibgaba ta fannin ilimi da lafiyar mata da kananan yara na guraren da abin ya shafa. Duk da cewa ba uzuri ba ne ga samari su shiga harka ta ta’addanci amma masana na alakantashi da rashin aikin yi da lalacewa kasar noma da karancin ruwa da ke kawo fari da fatara wanda hakan kan tilastawa wasu shiga karuwanci da sata da zamba domin samun abin duniya.

Dole ne gwanmantoci su zage damtse domin kawo hanyoyi da samari za su samu aikin yi da samar da yanayi mai kyau na noma da kayan noma na zamani domin ci gaban al’ummarta, abubuwa guda uku na zama bara zana ga ci gaban kowacce kasa sakamakon canjin yanayi wanda idan ba a samo hanyar rage radadinsu ba toh hakan na iya kawo tsaiko wajen samun ci gaba mai ma’ana ta fuskar ci gaban kasa; abu nafarko shi ne rashin kyakkyawar kasar noma, tsaro da kwararowar hamada, dole ne daukar mataki a kansu domin samar da ci gaba hakan kuma zai yiwune ta hanyar ilimantar da al’umma hanyoyi masu sauki da za su gane shin wai ta wacce hanya canjin yanayi zai zama illa ? idan ka dauki hamada  sakamakon sare itatuwa domin amfani da su don makamashi  da jin dumi, wannan al’ada tana da mutukar illa ga rayuwar jama’ar kasa baki daya domin wanna hanya ce da ke mayar da kasar noma tazama babu bishiya ko kuma bacewar daji daga inda aka san shi a da. Illolin ba za su misaltu ba kama daga rashin tsaro, yawan ficewar matasa zuwa cirani, cututtuka da suka shafi da fata, da ciwon idanu da sauransu kamar yadda muka sani shi ne lalacewar kasar tudu (dryland). wanda tana faruwa ne sakamakon abubuwa da dama kamar canjin yanayi daga Allah da kuma ayyuka ko mu’amalolin dan’adam na yau da kullum. Haka nan hukumar abinci da noma ta majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa kwararowar hamada ita ce babbar matsalar muhalli a duk fadin duniya inda suka fassara kwararowar hamada da kyakykyawra kasa ta koma sahara sakamakon saran bishiyoyi,fari, ko noman gona ba bisa ka’ida ba.

Rashin tsaro : Sakamakon rashin kyaun kasar noma da kafewar tafkuna yakan jawo cece-kuce da barazana da zaman lafiya na jama’ar Arewa maso gabacin Nijeriya kamar su Maiduguri , Adamawa da Yobe sakamakon rashin aikin yi da ke da alaka da tashe tashen hankula kamar yadda hakan ke faruwa a yankunan Sudan ta kudu Senegal da sauran kasashe masu tasowa duk hakan na nuna gazawa gwamnatocin Afurka da Asiya wanda hakan ke barazana da zamantakewa tsakanin al’umma daban daban. Koda kasashen da suka cigaba tasirin canjin yanayi na shafa harka tsaronsu da kuma tattalin arziki yayin da kasashe kamrsu Germany ke kokarin karbar ‘yan gudun hijira daga kasashe masu tasowa hakan ba yana nuna cewa suma sun wadata ‘yan kasarsu da duk bukatunsu nay au da kullum bane yayin da wasu ke murna da ‘yan gudun hijra wasu kuwa kulle kofarsu suke wanda hakan shi ke tunzura wasu su shiga ta’addanci sakamakon rashin sanin makomarsu a rayuwa wanda yaki da talauci shine ummul aba’is na faruwar hakan.

Fatara daYawan jama’a : Binciken masana ya alakanta yawan talauci dake damun kasashen Afurka nada alaka da Kwararar jama’a zuwa birane sakamakon  neman tsira ko samun abinsawa abakin salati yajawo gurbacewa muhalli sakamakon rashin shirin gwamnatocin akan yawan baki dake shiga birane batare da ka’idaba wannan yana jawo barazana ga rayuwar mazauna birni, yakamata gwamnatocin jahohi su samar da kayayyakin more rayuwa  a kauyuka domin rage kwararar baki zuwa birane.

Kowa ya san halin da duniya take ciki na karyewa tattalin arziki sakamakon dalilai masu yawa, kama daga faduwar farshin man fetur, yake yake da saurasu, talauci ba karamar cuta bace da tasami dan adam kuma tanada illoli dayawa dasuka shafi ingancin muhalli, domin talauci yana taimakwa wajen abubuwa da yawa na tabarbarewa muhalli, misali sa sare itace na da alaka da talauci domin yawancin mutane musamman manoma sun dogare da albarkatun gandun daji ne domin rayuwa a lokacin rani don samun abin da za su kula da iyalansu, wanda hakan na zama barazana ga kasar noma ta hanyar zaizayar kasa dake addabar kasashe masu tasowa , domin hanyace da kasar noma ke zaizayewa ta hanyar gudun ruwan sama, ko iska maikarfi da ke  kwashe saman kasar noma tamai da ita maras amfani, ko anyi shuka baza a sami wani abin kirki ba sakamakon kwashe sinadarai dake zama kamar taki ko kuma abincin da tsirai za su ci domin su girma.

Sakamakon talauci da muke da rashin wayewa sare itatuwa ya zama ruwan dare a kowanne bangare na wannan kasa tamu, wannan kuma yasamo asali ne domin gazawar gwamnati ta samar da makamashi na zamani akan farashi mai rahusa. Wannan babbar illa ce ga rayuwar dan’adam saboda haka ya zama dole gwanatocin jahohi da kananan hukumomi su samar da hanyoyi na ilimantar da jama’a a kan illolin sare itace, domin illolinsa nada alaka da kwararowar Hamada da zaizayar kasa wadda suma babbabr ilace ga rayuwar dan’adam.

 

Exit mobile version