Korayen tsaunukan yankin Tizi Ouzou na Aljeriya, masu lullube da lambun zaitun da bishoyi masu cikar ganye, yanzu wutar daji sama da dari ta lalata su cikin mako biyu.
Ana iya jin zafin wutar daga wuri mai nisan gaske.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti
- Waiwaye Game Da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida Ta Duniya
A wani gidan sayar da mai a lardin Bouira, wani mutum mai zuba wa ababen hawa man fetir ya wahala da yanayi ya sauya ya koma na tsananin zafi.
“Zafin na fitowa ne daga tsaunukan. Ban taba ganin wutar daji irin wannan ba,” ya shaida mana.
Wutar daji ba sabon abu ba ne a Aljeriya, musamman a yankin Arewa maso gabashi na Tizi Ouzou.
A iya cewa ma abu ne da aka saba gani akai-akai da masu aikin agaji ke fama duk shekara.
Kuma wutar dajin na yin darna mai dumbin yawa duba da rashin ruwan sama da iska mai karfin gaske da ke kadawa.
Dubban kadada a kusa da kauyukan Larbaâ Nath Irathen, Beni Douala da Aït Mesbah ne wutar ta mamaye ta kona bishoyoyin masu yawan ganye da a baya suke jere a kan tsaunukan.
Rahotannin farko-farko sun gano cewa wutar ta wannan shekarar ta yi barna ga dazukan Algeriya fiye da duka watar dajin da aka yi daga shekarun 2008 zuwa 2020 gaba daya.
Akalla mutum 90 sun mutu yayin kashe wutar ciki har da sojoji 33 da aka bai wa lambar yabo.
Duk da kokarin kashe wutar daji duk shekarar, da kuma ikirarin kasafin kudi na sojoji mafi yawa a Afrika, Aljeriya ba ta da jiragen sama na kashe wutar daji.
A maimakon haka, wasu ‘yan kananan jirage ne kirar Mi-26 da ke iya daukar bokiti mai girman lita 1,000 suka yi kokarin kashe wutar.
Don haka, dole gwamnati ta nemi agaji daga Tarayyar Turai kuma ran 12 ga Agusta, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aika masu da jirage biyu.
Mutanen kauyen Beni Douala sun shiga aikin kashe wutar da tebir da rassan bishiya da duk wani abu da suke da shi.
“Kila fasfo din sa ne ya lalace,” Fethi Fellah wani dan agaji ya fada cikin raha lokacin da aka tambaye shi ko ya ga jirgi kashe wuta.
“Baya ga ‘yan kwana-kwana, babu wand aya fito ya agaza mana,” ya ce a lokacin da yake karkatar da jerin motoci daga tsaunukan zuwa birnin Tizi Ouzou inda iyalai suka taru a wasu rumfunan agaji.
Daya daga cikin wuraren shi ne babban dakin taron Le Printemps da ke karbbar mutanen da suka tsere daga muhallansu.
Fuskokinsu sun cika da jajircewa da bacin rai a lokacin da suka fahimci su za su yi wa kansu komai.
“Hukumomi ba su agaza mana wajen tserewa ba, dole muka dogara da masu aikin sa kai da ke zuwa daga kauye zuwa kauye,” a cewar Ines, wata ma’aikaciyar sa kai.
“Hukumomin na da wani bangare na alhakin yawan mutanen da suka mutu. Duk shekarar muna samun wutar daji kuma har yanzu ba a dauki wasu matakai ba,” a cewarta.
Daga Firai Minista Aymen Benabderrahmane da Shugaba Abdelmadjid Tebboune sun ce wasu bata gari ne ke sa wutar dajin, sai dai kuma ba su ba da wata kwakkwarar hujja kan haka ba.
Sun zarfi kungiyoyin ‘yan aware a yankin kabyle a kusa da Tizi Ouzou kuma sun ce za su sake duba alakar diflomasiyya da Maroko wadda ta ke zargi da goyon bayan kungiyoyin.
Sai dai sun manta da cewa kasashen da ke kusa da yankin Mediterranean suna fama da wutar daji a makonnin baya-bayan nan ciki har da Turkiyya da Girka da Cyprus da Italiya da Faransa.
Mai yiwuwa sauyin yanayi a yankin da taka rawa wajen faruwar abubuwan da ke janyo wutar dajin.
Sai dai har yanzu dumamar yanayi ba ya cikin wani batu da ake tattaunawa a Ajeriya.
Kuma asarar rai da ta muhalli da ake samu sanadiyyar bala’o’i sun fara yawan da ba za a iya kawar da kai ba.
Wutar daji ba ita ce kawai alamar sauyin yanayi a Aljeriya ba.
Hamadar Sahara, wadda ita ce kashi 80 cikin 100 na kasar na kara girma.
Ta karu da kashi 10 cikin dari a shekaru 100 da suka gabata a cewar mujallar Journal of Climate.
Karuwar hamadar na toshe hanyoyin da makiyaya ke bi don sama wa dabbobi abinci kuma tana tursasa wa manoma kara hakar kasa don samun ruwa.
Ga al’ummun da dama can suke daga gefe-gefen hamadar, dumamar yanayi na kara jefa su cikin mawuyacin hali musamman a lokacin bazara.
Dalibai a lardin Adrar, misali, na cikin rukunin dalibai da ke baya-baya a kokarin makaranta a kasar, saboda ba a gina azuzuwansu don iya zama a lokacin tsananin zafin yankin ba.
A Algiers babban birnin kasar, rashin isasshen ruwa ya sa wasu sassan birnin ba sa samun ruwa a famfo sai na dan wani lokaci a wuni guda.
Shugaba Tebboune ya sanar da cewa za a samar da tashoshin cire gishiri daga ruwan teku guda uku don shawo kan matsalar.
Sai dai, idan ba a dauki sauyin yanayi da muhimmanci ba, sannan a sa manufofi kan muhalli, irin wadannan ayyukan za su samar da sauki ne kawai a gajeren zango.