Yayin da Shugaban Jam’iyyar PDP da gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, su ka koka da zargin yunkurin tafka magudi a zaben gwamnan jihar Ekiti, INEC ta ce zargin ba abin kamawa ba ne kuma ba gaskiya ba ne, domin ko da jami’in hukumar bai isa ya iya aikata magudi a zaben ba, saboda tsari da kuma matakan tsaron da a ka saka a zaben.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya fito karara ya mayar da martanin ya na mai cewa, babu wani ma’aikacin hukumarsa da zai iya yin magudi ko murde zaben gwamnan jihar Ekiti, kamar yadda wasu ke zargi. Mahmood Yakubu ya bayyana haka a cikin makon nan, yayin da ya ke ganawa da jam’iyyun siyasa a Cibiyar Zabe ta INEC a Abuja.
“Ina tabbatar mu ku da cewa tsarin zaben da mu ka shigo da shi ya wuce tunanin wani ko ma wane ne ya yi magudi ko ya murde sakamakon,” in ji shi.
Yakubu ya ce an dauki tsauraren matakan da zai iya cewa idan dai wani zai iya murde zaben, to rakumi zai iya shiga ta kofar allura ya fita.
“Zargin da wasu ke yi wai an kwafi katin rajista da kuma na’urar karanta katin kada kuri’a, wannan duk shaci-fadi ne kawai.”
Tun da farko a jawabin nasa, Yakubu ya fara ne da shaida wa shugabannin jam’iyyun da ya gana da su irin shirin da INEC ta yi na gudanar da zabukan cike gurbi a jihohin Bauchi, Katsina, Taraba da wasu wurare.
Daga nan sai ya gangara kan zaben gwamnan jihar Ekiti, da ya ce za a gudanar a rumfunan zabe 2,195 da ke cikin mazabu 177 a fadin jihar.
Ya ce dukkan fadin kananan hukumomin jihar 17 za a gudanar da zaben, wanda ya ce jam’iyyun siyasa 35 su ka za su shiga zaben.