Yayin da wasu ke daukar harkar fim a matsayin wata hanya na neman kudi kawai, daya daga cikin manyan dattijai a cikin masana’antar Kannywood Alhaji Dan Asabe Garba ko kuma Olala ya ce akwai wasu ayyuka da ba zai iya yi ba ko nawa kuwa za a ba shi.
A lokacin da zan shiga harkar fim, masoya,iyalai da ‘yan uwa sun so su hana ni saboda a nasu tunanin zan iya yin wani abinda zai iya zubar masu da mutuncinsu amma ganin ina matukar sha’awar harkar ya sa dole suka hakura na shiga amma da sharudda biyu, na farko shi ne ba zan taba fitowa a cikin shirin fim a matsayin Dan Daudu ba hakazalika ba zan fito a matsayin Kwarto ba.
- Na Samu Wata Harkar Da Ta Fi Sana’ar Fim Kawo Kudade -Ali Dawayya
- Ana Yi Wa ‘Yan Fim Kallon Malamai A Zamanin Baya -Ali Rabi’u Ali
Yanzu haka a kan wannan matsaya ya sa suka barni ina yin wannan harkar, saboda haka ko nawa wani zai bani a kan in karya wannan alkawari da na daukar wa ‘yan uwana da iyalina ba zan karba ba saboda mutunci ya fi komai in ji Dan Asabe Olala wanda ya shafe tsawon shekaru ana damawa da shi a masana’antar Kannywood.
Dangane da kalubalen da masana’antar Kannywood ke fuskanta a halin yanzu, Olala ya ce daga cikin kalubale da ke damun Kannywood akwai rashin jari wanda ya sa an samu karancin yin fina-finai ba kamar a kwanakin baya da za kaga ayyuka sun yi yawa ba,a wancan lokacin a kan hada karfi mutum biyu ko uku su shirya fim daya saboda za a kai fim kasuwa a sayar kowa a bashi kudinsa.
Amma yanzu saboda yadda aka koma fina-finai masu dogon zango da dama mutane basu da isassun kudaden da za su saka wajen shirya manyan fina-finai da ake shiryawa a yanzu, saboda haka da ace zan samu shugabancin wannan masana’antar zan mayar da hankalina kacokan wajen hada kan mambobin masana’antar ta Kannywood.
Sannan kuma in tafi wajen samo masu hannu da shuni domin su zo su zuba hannayen jarinsu a wannan masana’antar, zaka ga da dama mutane na sha’war zuba hannayen jarinsu a wannan masana’antar amma ba su san yadda za su yi ba ko kuma hanyoyin da za su bi wajen ganin ba su yi asarar kudadensu da su ka zuba a harkar ba.
Daga karshe Alhaji Dan Asabe ya shawarci matasa mata da maza da ke da sha’awar shigowa wannan masana’antar domin su fara harkar fim a kan duk wanda zai shigo ya tabbatar da cewar zai iya hakuri har zuwa lokacin da Allah zai nufi ya samu daukaka, domin kuwa a dare daya ba zai samu abin da yake so ba dole sai ya jajirce ya kuma yi hakuri kamar yadda wadanda yake gani sun samu daukaka suka yi kafin shima ya zama wani abu a Kannywood.