Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta amince da rage makin shiga jami’a zuwa 140 ko fiye da haka, a matsayin shi ne maki mafi kankantar da za a iya samun gurbin karatu jami’a ga wanda ya mallaka a shekarar karatu ta 2022/23 ta shiga jami’oi a fadin tarayyar Nijeriya.
Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Is-hak Oloyede ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi yayin da ake kaddamar da tsarin yadda al’amarin samun gurbin karatu na manyan makaratu zai kasance tare da ba da lambar karramawa da ya gudana a Abuja.
Oloyede ya ce maki 100 shi aka amince a matsayin mafi karancin maki ga wadanda ke bukatar zuwa makarantun fasaha da kimiyya da kuma kwalejojin ilmi. Wannan yana nuna ba an tilasta wa makarantun sai sun amince da hakan ba, suna iya kara nasu amma kar abin ya wuce misali.
Haka nan ma ya ce dole ne su manyan makarantu su tabbatar suna bin ka’idar da aka bayyana a matsayin yadda za su tabbatar da hakan lokacin da suke duba takardun dalibai masu bukatar shuga makarantunsu.
“Dukkan makarantu abu mafi kyau gare su shi ne na tabbatar da suna bin ka’idarta maki 140 wanda dole a same shi kafin samun damar zuwa jami’a. Wannan na nuna cewa babu jami’ar da za ta amince da kasa da maki 140.
“Ga jami’o’i 15 masu zaman kansu da suka bukaci tsakanin maki 120 da 130, su gane da cewa shi al’amarin maki 140 abin ya tsaya matsayin doka ka da a karya ta.
“Ba za a taba amincewa masu da maki 139, ba za a amince da hakan ba don haka a tabbatar da ana bin dokar sau da kafa yadda aka tanada “.
Wannan sabon tsarin kamar yadda hukumar ta bayyana zai ba masu son rubuta jarabawar su rubuta a wayiyionsu na tafi da gidanka.
Oloyede ya kara jaddada cewa hukumar tana kashe makudan kudade lokacin yin jarabawar shiga jami’o’I, wannan shi ya sa aka bullo da wannan sabon tsarin.
“Muna kallon abin da ya zarce tsari na BOYD, wani tsari ne da daliban da za su rubuta jarabawar su kawo wayoyinsu na tafi da gida. Tsarin yana rage yawan kudaden da ake kashewa, amma bai taimaka wa fasahar ilmi ta zamani. Za a kafa hukumar da za ta rika hukunta wadanda suka aikata laifi lokacin jarabawar da za a bullo da ita ta wayoyin tafi da gidanka.
Ya ci gaba da cewa, “Za mu samu hadin gwiwa da jami’an tsaro daban- daban kan aikata laifin da ya shafi fasahar sadarwa ta zamani lokacin gudanar da jarrabawar da za mu rika daukar nauyinsu saboda suna da masaniyar kan yadda dalibai suke aikata laifin.
“Haka nan ma yadda ake yin rajista lokacin da aka bude damar yin hakan, saboda a yi maganin yadda ake cuta lokacin da ake yin rajisatar.
Ga jarrabawar shiga jami’oi ta shekarar 2023, Oloyede ya bayyana cewar Umeh Nkechinyere ita ce wadda ta fi kowa kwazo daga cikin wadanda suka rubuta jarrabawar da maki 360.
Daga karshe hukumar ta gabatar da mutane 10 da suka fi kowa hazaka daga cikinsu akwai Aguele Stephen mai maki 358 da Ositade Oluwafemi mai maki 358 da Gbolahan Ayinde mai maki 357 da John Fulfilment mai maki 356 da kuma Chimdubem Ugonna mai maki 355.