Sauyawa, canzawa, da dai sauran wadansu kalmomi da suke bada ma’anar barin wani abu zuwa wani akwai dalilin ko dalilan da suke sa ana yin hakan, idan aka kalli ‘yan siyasa suke yi lokacin da aka shiga Kaka ko kuma hulotin siyasa.
Amma dai babbar magana ita ce lokuta da yawa su ‘yan siyasa sun fi yin hakan musamman ma idan lokacin babban zabe ya fara karatowa.
- CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Murnar Tsakiyar Yanayin Kaka Ta Yin Amfani Da AlAdun Haduwar Iyalai
- ’Yan Bindiga Sun Saki Mutane 43 Da Suka Sace A Masallaci, Sun Kashe Daya A Zamfara
Sai dai kuma da akwai rashin akidar siyasa wadda ita ce ke sa wasu ‘yan siyasa suke yin hakan abin ya hada da shi wani ko su wasu ‘yan siyasar bata Talakawa suke yi ba, suna duba kansu tun a karon farko.
Wasu daga cikin masu irin wannan akidar idan dai suka nemi wani mukami a siyasa basu samu ba.
To shikenan sai su yanke shawarar barin jam’iyyar siyasar da, aka san suna cikin ta tun shekara da shekaru su kuma wata tare da fatan wankin hula ba zai kai su zuwa dare ba.
Idan ana maganar akidar siyasa ita ce ko mai runtsi,ko wuya ko dadi ,a kada a raya kar mutum ya bar jam’iyyar da yake.
Wannan ana iya tunawa da Shugabannin siyasar jamhuriyya ta farko irin salon siyasa, da akidar da kowannen su yake da ita, bai fa barinta saboda wani dalili na kashin kansa kawai. Yana kallon al’ummar sa ne.
A Jamhuriyya ta farko irin jam’iyyun da suke tasiri sun hada da NPC, NCNC, NEPU, AG, sanin kowa ne suna da akida wadda suka yi amfani da ita.
Shugabanni kamarsu Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, Dakta Nnamdi Azikwe, Firimiya Ahmadu Bello Sardauna, Samuel Ladoke Akintola, Chif K.O Mbadwe, Malam Aminu Kano, Sir Kasim, Chif Obafemi Awolowa.
Babu wanda ya bar jam’iyyar da aka san shi da ita zuwa wata. Da haka haraka shigo jamhuriyya ta biyu jam’iyyu 1979 zuwa 1983 UPN, NPN, GNPP, PRP, NPP, hakanan suka tafiyar da al’amuran siyasar nasu tare da akida.
Bayan tsaikon da aka samu daga watan Disamba na shekarar 1983 zuwa shekarar 1999 da aka samu dogon lokacin da ba a yi siyasa ba, sabbin jam’iyyun da suka kasance sune ACN, PDP, APP wadda daga baya ta koma ANPP, APGA, da dai sauran jam’iyyu. Lokacin aka tsayar da Buhari dantakarar Shugaban kasa 2015 da bayan an zabe shi abubuwa da yawa sun faru, musamman masu nasaba da sauya jam’iyya zuwa wata da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bar jam’iyyar PDP ne ya koma APC can ma da bukatar sa bata samu ba ya kara komawa PDP, sannu a hankali shi ma ya barta domin bukatarsa ta kasancewa dan takara ya koma NNPP.
Kamar kunbo kamar katanta shi ma Sanata Ibrahim Shekarau ya bar PDP zuwa APC, sai NNPP har daga karshe dai ya sake komawa PDP.
Kamar dai dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar haka ya bar PDP zuwa APC da yake abin yaki ci yaki cinyewa sai ya koma PDP.
Idan dai ba a manta ba Sanata Bukola Saraki da Tsohon Ministan Sufuri Chibuke Rotimi Amechi, tsohon shugaban majalisar wakilai kafin ya zama gwamna Aminu Waziri Tambuwal da sauran wasu gaggan ‘yan siyasa suna irin wannan sauye- sauyen jam’iyya.
Shi sauyin jam’iyya kowa yana da na shi ra’ayi, wani manufar shi bai samun aiwatarwa, wani shugabanci yake kwadayi, wani taimakawa al’ummarsa yake son yi.
Ya lura kuma inda yake ba zai cimma burin shi ba sai ya sauya jam’iyya, yayin da wasu suke shiga da sa a wasu gara jiya da yau haka dai al’amarin yake kasancewa.
Koda yake dai shi wannan al’amari na sauya jam’iyyar siyasar da wasu ‘yan siyasa ko shakka babu suna kwashewa da mara be domin kuwa idan ba su samun hakan, ko mafarkin yin hakan ma ba za su yi ba.
Sun kuma san suna da magoya baya ne wadanda duk inda suka nufa suna binsu, kamar dai irin manyan ‘yansiyasa wadanda Talakawa ke karuwa da su.
Muna iya duba Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya taimakawa ‘ya’yan Talakawa lokacin da yake gwamnan Jihar Kano har ma daya rike mukamin Minista da kuma Sanata, hakan shi ma Sanata Ibrahim Shekarau tare da sauran ‘yan siyasa kowa ya san irin gudunmawar da yake ba magoya bayansa ko lokacin siyasa, ko kuma akasin hakan taimaka masu yake yi.
Irin haka ce ta sa wasu ‘yan siyasar sun san irin amfanar da suke samu daga wurin ‘yan siyasa wadanda suke goya ma baya, duk abinda suka ce ma Talakawan su yi a shirye suke su yi.