Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Borrusia Dortmund da ke buga babbar gasar Bundesliga ta ƙasar Jamus Edin Terzic ya bayyana aniyarsa ta ajiye aikinsa na horar da ƙungiyar bayan shafe shekaru biyu.
Terzic ya lashe kofin DFB Pokal a shekarar 2022 tare da Dortmund kafin ya jagorance su zuwa wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai na bana da suka buga da Real Madrid a filin wasa na Wembley Stadium da ke birnin Landan.
- Yaushe Za A Fara Kofin Duniya Na Kungiyoyi?
- Kayayyakin Wasanni Kirar Kasar Sin Sun Samu Yabo A Gasar Wasannin Afirka Ta 13
Babu wata rashin jituwa tsakanin Terzic da mahukuntan ƙungiyar, kawai dai ya yanke wannan shawarar ne a ƙashin kansa Dortmund ta bayyana a shafinta na sada zumunta.
Ana hasashen tsohon ɗan wasan Dortmund Nuri Sahin ne zai jagoranci ƙungiyar a wasannin sada zumunta a matsayin kocin rikon ƙwarya yayinda zai nemi wadanda zasu taimaka masa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp