Koeman Ya Zama Mai Koyar Da Kasar Holland

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Holland ta nada tsohon mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Eberton, Ronald Koeman, a matsayin mai koyar da  tawagar yan wasan kasar, kan yarjejeniyuar shekara hudu da rabi.

Rabon da Koeman mai shekara 54 ya horar da wata kungiyar kwallon kafa tun cikin watan Oktoba, bayan da Eberton ta sallame shi daga aiki sakamakon kungiyar takasa buga abin arzuki a karkashinsa.

Koeman zai maye gurbin Dick Adbocaat wanda ya kasa kai kasar Holland din gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a bana.

Wannan ne aiki na 10 da Koeman zai yi a matsayin mai koyarwa, bayan da ya horar da Bitesse Arnhem da Ajad da Benfica da PSB Eindhoben da Balencia da AZ Alkmaar da Feyenoord da Southampton da kuma Eberton.

Koeman ya yi wa Holland wasa 78, yana daga cikin wadanda suka dauki kofin nahiyar Turai a shekarar 1988, a lokacin da kasar take da fitattun ‘yan wasa da suka hada da Ruud Gullit da Frank Rijkaard da kuma Marco ban Basten.

Haka kuma ya buga wa kungiyoyi da suka hada da Barcelona da Ajad da kuma PSB wasanni inda nanma ya lashe kofuna da dama a kungiyoyin.

 

Exit mobile version