Hukumar raya Kogin Rima da ke Sakkwato ta jaddada kudurinta na bunkasa hanyoyin noma domin kawar da fatara da haɓaka tattalin arzikin yankin Arewa da Nijeriya baki daya.
Hukumar ta bayyana cewar za ta gudanar da muhimman tsari domin samar da shiri mai dorewa na zuba jari a harkokin noma a matsayinsa na ginshikin bunkasa tattalin arziki tare da kawar da fatara a cikin al’umma.
- Ana Zargin Wani Ɗansanda Da Kisan Wata Mata Kan Cin Hancin Naira 2,000 — Bincike
- Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Kisan Mafarauta A Jihar Edo
Sabon shugaban hukumar, Abubakar Malam ne ya bayyana hakan a jawabinsa na kama aiki a inda ya bayyana cewar, manufar hukumar shi ne bunkasa samar da abinci, rage fatara, aiwatar da shirye-shirye domin farauto masu zuba jari mai dorewa a yankunan karkara da inganta jin dadin al’ummar yankin.
Abubakar Malam wanda shine Shettiman Gwandu, ya ce akwai babban aiki a gaban su domin wajibi ne su ɗaura ɗamarar dawo da kima da martabar hukumar, bin ka’idojin aiki, karfafawa ma’aikata, jajircewa da aiki tukuru tare da haɗin kai domin samun kyakkyawan sakamako.
Ya ce “Wannan hukuma ce mai matukar muhimmanci tun daga tushe, don haka, wajibi ne mu tabbatar da haɗin kai mai ɗorewa domin ɗora ayyukan hukumar a hanya mai kyau domin bunkasa jin daɗin al’ummar jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Katsina da ke karkashin hukumar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp