Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu bayan da wani kogon hakar ma’adinai ya rufta da masu hakar ma’adinan a dajin Yadagungume da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi a ranar Asabar.
LEADERSHIP ta samu cewa, masu hakar ma’adinan sun rasa rayukansu ne a yayin da suke tono ma’adinin ‘Lead’
Wani wanda lamarin ya faru a gabanshi wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, masu aikin hakar ma’adinan sun shafe watanni suna aikin hakar ma’adinin.
Ya tabbatar wa Wakilinmu cewa, an ciro gawarwakin ma’aikatan hudu acikin kogon da ya rufta musu.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, kantoman karamar hukumar Ningi, Hon. Ibrahim Zubairu, ya ce, mutanen hudun sun makale ne a kogon ne, daga bisani kuma suka Mutu kafin kai musu daukin gaggawa.
Zubairu ya ce, wurin hakar ma’adinan yana dajin Kogo Kadage ne mai nisan kilomita bakwai daga garin Yadagungume.