Daga Yusuf Shuaibu
A ranar Talatar da ta gabata ne Babban bankin Nijeriya (CBN), ya bayar da tallafin sama da Naira miliyan 234 a bangaren bincike ga wasu mutane biyar da suka ci gajiyar shirinsa na kula da kiwon Lafiya da cigaban tsarin lafiya.
Wadanda suka samu tallafin sune, Farfesa na ‘Epidemiology’, Olufemi Babalola, wanda ya samu tallafin Naira miliyan 50, Farfesan ‘Microbiology’, Ikechukwu Okoli, daga Jami’ar Nnamdi Azikiwe, wanda shi ma ya samu tallafin Naira miliyan 50.
Sauran sune, Dakta Garba Bubah daga kwalejin fasaha ta jihar Jigawa, wanda ya samu tallafin Naira miliyan 42.1, yayin da Dakta John Ogedemgbe daga Jami’ar Abuja, da Dakta Otega Ejofodomi, malamin injiniyancin lantarki daga Jami’ar tarayya ta albarkatun man fetur, sun samu Naira miliyan 50 da kuma Naira miliyan 42.4.
Sakataren Gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, a cikin sakon fatan alheri a wajen taron, ya yaba wa CBN kan bayar da tallafi ga bangaren kiwon lafiya, musamman a lokacin barkewar cutar Korona.
Mustapha, wanda har ila yau shi ne Shugaban Kwamitin tsaro na fadar Shugaban kasa kan cutar korona, ya ce, HSRDIS na daga cikin manufofin babban banki game da annobar korona.
Ya kara da cewa, wannan shawarar ita ce ta taimaka wajen karfafa tsarin kula da lafiyar jama’a na Nijeriya tare da samar da kudade na zamani zuwa sabbin ingantattun magunguna, alluran riga-kafi da kuma yaki da cututtuka masu yaduwa.
“Cutar korona ta zo da mummunan sakamako da illa, amma kuma ta ba mu dama don sauya tsarin samar da lafiyar mu. Wannan HSRDIS din ta CBN za ta fassara ne zuwa kafa manyan cibiyoyi ta yadda idan muka sake fuskantar wata annoba, al’ummomi masu zuwa za su ci gajiyar wadannan cibiyoyin. Ina godiya ga Gwamnan CBN da tawagarsa game da wannan shirin, wanda ya zo a lokaci mafi dacewa irin yanzu,” in ji Boss Mustapha.
Gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele, ya bayyana, cutar ta fallasa raunin tsarin kiwon lafiya na Nijeriya.
Emefiele ya ci gaba da cewa, ingantaccen wurin aiki da lafiya ya zama dole ne don ci gaba da bunkasa tattalin arziki gami da kwanciyar hankali na tsarin kudi.
Ya bayyana kiwon lafiya a matsayin tubalin ci gaban kowace kasa, wanda ya cancanci samun isassun kudade domin gudanar da bincike da ci gabanta.
“CBN, tare da Gwamnatin tarayya, sun yanke shawara akan cewa dole ne mu fara duba ciki mu samarwa kanmu. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa CBN ya kafa kungiyar Kwararrun, karkashin jagorancin Farfesa Mojisola Adeyeye, Shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna, don jagorantar HSRDIS din. Mayar da hankali kan bincike da ci gaba a kasashen da suka ci gaba ya taimaka wajen samar da riga-kafin cutar korona,” in ji shi.
Emefiele ya kara da cewa, an samu shawarwari sama da 200 wanda daga ciki 68 an ba su maki, kuma an zabi guda biyar mafi kyau.
Ya ce, shirin zai samar da tallafi don ba da damar gudanar da bincike da ci gaba a cikin alluran riga-kafi da magungunana na cutar da sauran cututtuka.
Ya yi kira ga sauran cibiyoyin kamfanoni da su hada kai da CBN don samar da bincike da ci gaba don amfanin dukkan ‘yan Nijeriya, yayin da ya bukaci wadanda aka karba da su yi amfani da tallafin yadda ya kamata.