A yayin da Nijeriya ta tsunduma cikin karayar tattalin arziki a karon na biyu cikin shekaru biyar, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa annobar cutar Korona ce ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya kaca-kaca; Buharin ya bayyana hakan ne a yayin taron Tattaloin Arziki karo na 26 da ake gudanarwa yau Litinin a Abuja.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya wakilci Shugaban Kasan a taron. Inda ya bayyana cewa; kulle da aka yin a watanni ya sa ko noma ba a samu damar yi ba, harkokin kasuwanci, makarantu, otal-otal da gidanje cin abinci duk an kulle. Kai hatta jigilar jiragen sama da ta motoci duk sun samu tsaiko sakamakon annobar.
Osinbajo ya bayyana cewa harkokin tattalin arziki za su iya daukar tsawon shekara uku kafin su dawo daidai, shiyasa ma gwamnatinsu ta fito da tsare-tsare na farfado da tattalin arzikin kasa, wanda mafi yawan tsare-tsaren a cewarshi ‘yan kasa ne za su amfana, musammam ma dai masu karamin karfi.