Daga Rabiu Ali Indabawa,
Wata Kotun Majistare da ke Ota, Jihar Ogun a ranar Laraba, ta ba da umarnin a tsare wasu abokai biyu a gidan gyara hali, bisa zargi da yi wa wata yarinya, ‘yar shekaru 19 fyade. ‘Yan sanda sun tuhumi Oluwadamilare Oyeniyi, mai shekaru 30, da Okoriji Emmanuel, mai shekaru 30, da aikata laifuka biyu na hadin baki da aikata fyade.
Alkalin kotun Shotunde Shotayo, wacce ba ta amsa rokon Oyeniyi da Emmanuel ba, ta umarci ‘yan sanda su mayar da fayil din karar zuwa Daraktan Lauyoyin Masu Gabatar da Jama’a na Ogun don neman shawara kan shari’a. Shotayo ya dage sauraron karar har sai 5 ga Maris. Tun da farko, Lauyan Gwamnatin, Oluwole Ayede ya fadawa kotun cewa Oyeniyi da Emmanuel sun aikata laifin ne a ranar 12 ga Disamba 2020 a gidansu dake Ota Jihar Ogun. Ayede, ya yi zargin cewa Oyeniyi da Emmanuel sun hada baki suka yi wa yarinyar fyade.
Ya kuma yi zargin cewa an kama Oyeniyi da Emmanuel yayin da suke daukar faifan bidiyo na laifin da suka aikata. A cewarsa, laifin, ya ci karo da sashe na 358 da 516 na Bol.1 Code na hukunta masu laifi, Code Bol.1, Laws na Jihar Ogun, 2006. NAN
Mai shekara 30 mai suna, Tajudeen Monsuru, ya amsa laifin da ake zarginsa na amfani da sassan jikin mutum tare da yin tsafi tare cin naman yana korawa da ruwan giya duk lokacin da yake cikin nishadi. Da ya ke amsa tambayoyin ‘yan jarida lokacin da hukumar ‘yan sanda ta yi holinsa shi da wasu masu laifin a hedkwatarsu dake Osogbo cikin jihar Osun, ya ce suna aikata hakan ne shi da budurwarsa ce da mai suna Alan Mutiyat.
“Muna kashe mutane ne bayan sun aminta da mu. Mafi yawan lokuta har bacci muke yi tare kafin cikin dare mu kashe su mu yi gunduwa-gunduwa da su don sayar da sassan jikinsu.