Babbar Kotun Tarayya ta daya da ke Yola a Jihar Adamawa, karkashin jagorancin mai shari’a A.M. Anka, ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar APC wanda ya samar da Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, Aishatu Dahiru Binani, a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar a zaben 2023.
Mai shari’a Anka ya ce jam’iyyar ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023 a jihar, saboda bai bayar da umarnin sake sake zaben fidda gwani ba.
- Abin Da Ya Sa Manoman Doya A Jihar Taraba Ke Tafka Asarar Miliyoyin Naira
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Kafuwar Cibiyar Kasa Da Kasa Ta Bunkasa Kirkire-Kirkire Da Ilimi Domin Wanzar Da Ci Gaba A Fannin Sufuri
Idan za a iya tunawa cewar Binani ce ta lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022, inda ta samu kuri’u 430 wanda ta kayar da abokin hamayyarta Nuhu Ribadu wanda ya samu kuri’u 288; da kuma tsohon gwamnan jihar, Umaru Bindow wanda ya samu kuri’u 103; sai Hon. Abdulrazak Namdas wanda ya samu kuri’u 94, Safari Theman ya samu kuri’u 21, Umar Mustapha ya samu kuri’u 39.
Kotun ta kuma ce jam’iyyar ba za ta shiga zaben gwamna na 2023 ba, saboda haka ta gargadi Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani da kada ta bayyana kanta a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Adamawa.
Mai shari’a Anka a lokacin da ya ke yanke hukunci a ranar Juma’a, ya ce an yanke hukuncin ne kan rashin bin ka’idojin jam’iyyar da kuma kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya a zaben fidda gwanin.
Ribadu, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwanin, ya maka ‘yar takarar gwamnan, Aishatu Binani, APC da INEC a gaban kotu.
Ya kuma bayar da shawarar soke zaben fidda gwanin da aka yi, inda ya yi zargin an tafka kura-kurai a lokacin zaben fidda gwanin.