Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna, ta soke zaben fidda gwanin da jam’iyyar PDP ta gudanar a mazabar Kaduna ta tsakiya sakamakon wasu kurakurai.
Kotun ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani na dan takarar Sanata na jam’iyyar a cikin kwanaki 14.
- An Mayar Da Tubabbun Mayakan Boko Haram 3,500 Unguwanninsu A Jihar Borno
- Rashin Tsaro: Buhari Ya Kalubalanci ‘Yansanda A Kan Matsalar Tsaro
Mai shari’a Muhammed Garba Umar na babbar kotun tarayya da ke Kaduna, wanda ya yanke hukunci a ranar Laraba a kan shari’ar ya ce “Duk korafe-korafen da mai shigar da karar ya yi na da yawa, haka ma hukuncin da INEC ta yanke na gudanar da sabon zaben fidda gwani da ba a yi ba daga baya, kamar yadda sakamakon ya gudana, ikirarin da wanda ake tuhuma ya yi watsi da shi.”
Mai shigar da karar, Usman Ibrahim, ta bakin lauyansa, Samuel Atung, (SAN), ya garzaya kotu yana kalubalantar fitowar Lawal Adamu a kan rashin kuri’ar da aka kada masa, inda ya roki kotun da ta rushe wannan zaben tare da bai wa duk wani mai bukata dama daidai gwargwado don gwada farin jininsa.
Atung ya bayar da hujjar cewa wanda yake karewa yana da faifan bidiyo da bayanan da suka nuna cewa wakilai sun kada kuri’a wadanda sakamakon shari’ar da ya yi nuni da su shi ne rushe sakamakon zaben fidda gwanin da kuma soke sakamakon zaben, inda ya kara da cewa majalisar zartaswar jam’iyyar PDP ta kasa ta nemi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
Hukumar INEC ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani kawai don wanda ya karewa ya tattaro mabiyansa zuwa wurin da aka yi zaben a banza.
Lauyan Usman Ibrahim, Samuel Atung, (SAN) da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, ya tabbatar da cewa kotun ta zartar da hukunci ne bayan nazari da ta yi.
Atung ya ce, “Bayan da jam’iyyar PDP ta Kaduna ta tsakiya ta zabi dan takararta a zaben 2023, abokin takararmu ya rubuta koke ga kwamitin daukaka kara na jam’iyyar yana kalubalantar sakamakon zaben.
“Muna da hujjojin bidiyo kan hakan kuma kwamitin ya yi la’akari da rokon da muka gabatar kuma ya mika shawararsa ga kwamitin zaben wanda a cikin hikimarsa ya yi kira da a sake zaben fidda gwanin.
“Jam’iyyar PDP ta rubuta wa INEC wasika, ta sanar da ‘yansandan Nijeriya, jami’an tsaron farin kaya da sauran masu ruwa da tsaki game da matakin da ta dauka na sake gudanar da zaben fidda gwanin na shiyyar Sanata Kaduna ta tsakiya, wanda abin farin ciki ne.
“Abin takaici a ranar da aka saka, abokin aikinmu, bayan ya tattaro magoya bayansa zuwa wurin da za a sake zaben fidda gwanin, sai aka ce ba za a ci gaba da gudanar da zaben ba saboda yadda mahukuntan suka ba da umarni.
“Mun zo kotu ne muna neman adalci a wannan takin kuma alkali ya yanke hukuncin cewa jam’iyyar ta bi matakin da kwamitin kasa ya dauka sannan ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwanin nan da makonni biyu.”